Me Dan Kasa Ya Amfana Da har Zamuzo Muna Bikin Cikar shekara 61 A Nigeria Inji Cewar?

Ministan harkokin cikin gida Rauf Aregbesola ne ya sanar da hakan a madadin gwamnatin tarayyar.

A jiyane ministan har kokin Cikin gida Ya taya ‘yan kasar murna yana mai cewa gwamnati ta mayar da hankali wajen kawo karshen dukkan kalubalen da kasar ke fuskanta.

“Kasa mai yawan al’umma kusan miliyan 200 kuma mutanen sun kasance masu basira da kwazo, kuma masu haskawa tamkar daiman. wato matsayin yawan shekarun da kasar ta kai.

“‘Yan Najeriya na sheki tamkar daiman a cikin kwali, daga wadanda suke bangaren ilimi zuwa kasuwanci da kirkire-kirkire da wake-wake da fina-finai da nishadi da ado da al’adu.

“Mu ne kasar Afirkan da ke kan gaba a duniya kuma abar alfahari nahiyar Afirka,” a cewar Aregbesola.

Najeriya ta samun ‘yancin kai daga Turawan mulkin mallaka ne ranar 1 ga watan Oktoban 1960.

Ministan ya jaddada cewa murnar cikar shekara 61 da samun ‘yancin Najeriya na da muhimmanci, amma lafiyar ‘yan kasar ce gaba da komai a wajen shugaban kasa, musamman ma a wannan lokaci da ake damuwa kan yadda cutar korona nau’in Delta ke ci gaba da bazuwa a kasar.

Don haka ya ce a bana ba za a yi wasu bukukuwa kamar yadda aka saba ba.

Aregbesola ya yi amfani damar wajen yi wa ‘yan Najeriya fatan yin bikin wannan rana lafiya.

Ya kuma tunasar da ‘yan kasar kan abin da gwarazan da suka yi gwagwarmayar karbo ‘yanci suka fada, na cewa duk da bambancin addini da yare da al’ada sun ajiye komai a gefe suka yi gwagwarmayar samun ‘yancin kasar tare.

A karshen sanarwar ya ce “dole mu yi aiki tare don ci gaban Najeriya,” in ji Aregbesola.

Rahotanni sun ce an fara bukukuwan murnar ranar ne tun ranar Lahadi 26 ga watan Satumba da yin addu’o’i a babban cocin kasa da ke Abuja.

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da matarsa sun halarci taron da sauran manyan shugabannin addinin kirista.

 

Da wannan nakawomuku karshen rehotan Kuna tare Dani A.Usman Ahmad a shafinmu na Dalatopnews.

Kada kumanta kudanna Mana alamar kararrawar sanarwa Domin samin Jin kararrawar shirye-shiryanmu masu kayatarwa mungode

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button