Advertisement

Hedikwatar Tsaro ta Nigeria ta bayyana Dalilin dayasa ta kashe wasu masu su a Jihar Barno.

 Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Hedikwatar tsaro ta Najeriya tayi karin haske game da kashe wasu masu su da sojoji suka yi a jihar Borno.

A safiyar yaune muka Sami wani rahotan daga shafin legit.ng hausa Wanda muka tsinkayi  wani saban labari Wanda kungiyar sojojin Nigeria tayi Karin haske akan mutanan da suka kashe a barno.

Wanda I Dan Baku mantaba a makon da yagabata muka sanar daku wannan rahotan daga shafinmu na Dalatopnews.

GA KANUN LABARAN:

Hedikwatar tsaro na kasar watau DHQ tace ta hallaka ‘yan ta’addan ISWAP ne da suka fake da kamun kifi, suna yin ta’adi a yankin tafkin Chadi.

A wani jawabi da hedikwatar ta fitar ta bakin darektan harkokin yada labarai, Birgediya-Janar Benard Onyeuko, ta bayyana ainihin abin da ya faru. Birgediya-Janar Benard Onyeuko yace sojoji sun gano ‘yan ta’addan suna yin shigar masunta, su dauki wasu kaya a cikin jiragen ruwa a gabar rafin.

Jami’in sojojin kasar yace sun gano wadannan mutane ba kama kifi suke yi ba, suna ta jigilar wasu kaya da ba a san menene ba, suna yin gaba da su.

Jaridar ta rahoto Janar Benard Onyeuko yana cewa har yanzu ba a halasta kamun kifi a yankin ba.

“Hankalin hedikwatar tsaro ya zo ga wani karkataccen labarai da yake yawo a kafafen sadarwa na zamani cewa OPHK ta kashe masunta 20 da ke kiwon kifi a wani hari ta jirgin sama a Kwatan Daban Masara a ranar Lahadi, 26 ga watan Satumba, 2021, a kusa da yankin tafkin Chadi a Arewa maso gabashin Najeriya.”

Akasin abin da aka rahoto, sojoji sun gano ‘yan ta’addan ISWAP ne, ba masunta ba.

Kada kumanta kuna tare Dani A.Usman Ahmad Dauke da Labaran Duniya.

KU KARANTA WANNAN:

 

Kalli Kwalliyar Jaruman Kannywood Na Taya Murnar Nigeria Samun ‘Yanchin Kai Na Shekara 61

 

Fatima Ali Nuhu Ta Nuna Alamun Sha’awa/Gaskiyar Magana Akan Hatsarin Ado Gwanja Da Adam A Zango

 

Bude layikan waya a yakin Zamfara Gwamnatin Jihar ta sanar da budewa a Cikin Gusau Babban birnnin jihar

 

 

 

 

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button