An Sami nasarar cafke Gawurtattan Dan ta Addan da ya gagara a yakin zamfara dakuma kananun Yan Bindiga mutun 21 a yankuna maban banta.

Rundunar ta ƴan sandan Jihar Zamfara ta ce ta kama gawurtattun ƴan bindiga 21 a wurare daban-daban na jihar sannan sun kashe wasu guda biyar. bayan sabbin matakan tsaroda gwamnati ta ɗauka.
A safiyar yau mukasamu wani rahotan daga Daya daga Cikin manema labaranmu na yakin zamfara Wanda ya shaidamana cewa ‘yansandar Jihar zamfara sunkama wani gawurtattan Dan ta Adda.
Bayan bin rahotan Dan tabbatar da gaskiyane al’amari saimuka cikaro dacewa ‘yansandan ba iya shi suka kamaba harda wasu tsirari a yanki saban saban.
GA KANUN LABARAN:
Daga cikin waɗanda aka kama akwai babban kwamandan ƴan bindiga Bello Rugga da aka fi sani da sunan Turji wanda ya addabi mutane a dajin ƙaramar hukumar Gummi.
Ƴan sandan sun ce sun kama makamai a hannunsa da suka hada da bindiga ƙirar AK47.
Haka kuma, ƴan sandan sun ce sun daƙile hare-hare huɗu tare da kuɓutar mutane sama da 200 da ke hannun ƴan bindiga a wurare da dama kuma tuni suka koma wurin danginsu.
Rundunar ƴan sandan ta jihar Zamfara ta ce dalilin sabbin matakan tsaron, sauran manyan laifuka da ake aikatawa a jihar kamar fashi da makami da ƙwace mota da sata da dai sauransu sun ragu sosai.
Ku cigaba da bibiyarmu a shafinmu na Dalatopnews Domin samin sababbin labaran Duniya.
Ni A.Usman Ahmad ke Dauke da Labaran Duniya a daidai wanan lokacin a shafinmu na Dalatopnews kada kumanta kudanna Mana alamar kararrawar sanarwa Domin samin Jin kararrawar shirye-shiryanmu masu kayatarwa.
KU KARANTA WANNAN:
Ni Ba Musulmi Bane Amma Nasan Annabi Muhammad Yafi Kowa Daraja – Chicharito Hernández
Jerin jaruman kannywood mata guda 10 mafiya kyau a wannan shekarar ta 2021
Kada ku Manta kuyi subscrib na wannan site din Dalatopnews Domin samin Jin kararrawar shirye-shiryanmu masu kayatarwa mungode.