Masha Allah Mota Ta Kashe Wanda Yayi Zanen Batanchi Ga Annabi Muhammad (SAW) A Kasar Sweden

Subahannallahi Wani La’anannen Kafiri Dan Kasar Sweden Wanda Yayi Zanen Batanchi Ga Annabin Rahama Muhammad (SAW) Yadda Yayi Zanen Gangar Jikin Kare Da Sunansa, Allah Ya Jefa Masa Masifar Hatsarin Mota Ta Hallakashi Kamar Yadda Kafar Yada Labaran Kasar Ta Wallafa.

Kamar Yadda Rohotonni Suka Bayyana Sunan Mutumin Lars Vilks, Yana Tafiyane Acikin Motar Yan Sanda Marar Fenti, Yayi Hatsarin Da Wata Babbar Mota A Kusa Da Garin Markyard Dake Kudanchin Sweden.

Sannan Daga Wasu Majiyoyin Sun Bayyana Cewa A Yayi Wannan Hatsarin Da Lars Vilks Yayi Har da Wasu Yan Sanda Biyu Sannan Kuma Direban Motar Dasukayi Hatsarin Tare Ya Jikkata.

Vilks mai shekara 75 yana ƙarƙashin kulawar ƴan sanda sakamakon barazanar da ya yi ta fuskanta bayan yin zanen ɓatancin.

Zanen wanda aka wallafa a shekarar 2007, ya harzuƙa Musulmai da dama wadanda suke ganin duk wani zane da za a yi na fiyayyen halittar saɓo ne. Ya yi zanen ne shekara ɗaya bayan da wata jaridar ƙasar Denmark ta wallafa zane-zanen Manzon Allah.

Baya da Haka Ƴan sanda ba su bayyana sunayen wadanda suka mutu a hatsarin na ranar Lahadi ba, amma budurwar Vilk ta tabbatar da mutuwar tasa ga jaridar Dagens Nyheter.

Sanna Wata Sanarwa Daga Bakin Yan sandan Sunce har yanzu ba a san yadda hatsarin ya faru ba amma dai alamu sun nuna ba wani ne ya kitsa shi ba.

Zanen ɓatancin ya jawo tashin hankali har sai da firaministan ƙasar na wancan lokacin Fredrik Reinfeldt ya gana da jakadu 22 na ƙasashen Musulmai, a wani ƙoƙari na yayyafa wa lamarin ruwan sanyi.

Jim kaɗan bayan hakan ne, ƙungiyar al-Qaeda da ke Iraƙi ta sanya tukwicin dala 100,000 ga duk wanda ya kashe shi.

A shekarar 2015, Vilks ya halarci wata muhawara kan ƴancin faɗin albarkacin baki inda aka kai harin bindiga a birnin Copenhagen. Ya ce mai yiwuwa shi aka so kashewa a harin, wanda ya yi sanadin mutuwar wani daraktan fim.

Watana Yunin 2021 ma mai zanen shaguben nan a jarida dan kasar Denmark Kurt Westergaard, wanda aka fi saninsa saboda zanen da ya yi na Annabi Muhammad (SAW) wanda ya janyo ce-ce-ku-ce, ya mutu.

Ya mutu yana da shekarun 84 bayn ya sha fama da jinya, kamar yadda iyalansa suka shaida wa jaridar Berlingske.

Zamu So Mu Karbi Ra’ayoyinku A Sashenmu Tsokaci Akan Wannan Abu Daya Faru.

Ku Karanta Wannan Labarin:

Kasar Nigeria Bata Taba Samun Shugaba Nagari Kamata Ba Cewar Muhammad Buhari

Ku Karanta Wanna Labarin:

Jama’a da dama sun fashe da kuka yayin da diyar Sheikh jaafar mahoud adam malama Zainab take jawabi a jihar Kano

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button