Tirkashi Shin Kunsan Dalilin Dayasa Facebook, Whatsapp Da Instagram Suka Tsaya Da Aiki?

Kamar Yadda Kuka Sani A Yaune Litinin 4 Ga Watan 10 A Shekara Ta 2021, Manyan Shafukan Sada Zumuntar Zamani Wato Facebook, Whatsapp Da Instagram Suka Tsaya Da Aiki.

Shafukan Sun Tsaya Da Aiki Ne A Manyan Kasashen Duniya Kamar Su Washington, London Da Sauran Manyan Kasashen Duniya Ciki Kuwa Harda Kasar Nigeria Da Kasashen Africa.

Wannan Katsewar Da Wadanann Kafafen Sada Zumuntar Sukayi Ya Janyo Tsayawar Al’amura Ga Sauran Manyan Kamfanoni Da Suke Amfani Da Shafukan.

Sannan Kuma Wadannan Sune Manyan Kafofin Sadarwar Da Ake Tallace-tallace Da Sauran Abubuwa Domin Ci Gaba Ga Rayuwar Dan Adam.

Amma A Wani Guntun Bayani Da Muka Samu Daga Wajen Wani Ma’aikaci Na Shafin Facebook A Twitter, Ya Bayyana Cewa Sun Samu Matsalar Ne Bada Jimawa Ba Kuma Suna Kan Gyarawa Cikim Gaggawa.

Toh Allah Ya Kyauta Zamu So Mu Karbi Ra’ayoyinku A Sashenmu Na Tsokaci Akan Wannan Babbar Matsalar Data Shigo.

 

Ku Karanta Wannan Labarin:

Yadda Masu Garkuwa Da Mutane Sukayi Mana Fyade Nida ‘Yata Da Mijina Saurari Labarin Wata Mata

 

Ku Karanta Wannan Labarin:

Wasu tsofaffin jaruman kannywood mata da auren su yayi albarka har ma suka cimma wani matsayi

 

Ku Karanta Wannan Labarin:

Kasar Nigeria Bata Taba Samun Shugaba Nagari Kamata Ba Cewar Muhammad Buhari

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button