Wani magidanci ya yiwa likitan duba lafiyar fata dan banzan duka dalilin ya yaba kyawun fatar matar sa

‘Yan sanda a kasar Rasha sun kama wami mutumi wanda ya yiwa likitan duba lafiyar fata gukan tsiya, dalilin ya yaba kyawun fatar matar sa.
Matar mutumin da aka duba lafiyar fatar ta har ma likitan ya yaba fatar tata ta kasance musulma, inda ta sanar da mijin nata mai suna, Bakhriddin azimov cewa likitan fatar mai suna, Vladimir zhirnokleev ya yaba kyawun fatar ta.
Daga nan ne mijin matar ya kaiwa likitan farmaki inda ya masa dan banzan duka, inda a yanzu haka yana karfar hukunci kan wannan cin zarafin da yayi, kamar yadda shafin Hausaloaded ta ruwaito.
Karanta wannan labarin
Hotunan tsohon gwamnan jihar gombe sanata dan Juma goje tare da amaryar sa hajiya Aminatu dashiru
Kamar yadda RT ta bayyana, wannan al’amarin ya faru ne a ranar Talata 21 ga watan satumba a Nizhnevartovsk dake siberia.
Likitan ya bayyana cewa, ya duba lafiyar fatar matar ne kawai inda ya umarci matar data nuna masa hannun ta da cikin ta da kuma bayan ta amma bai umarce ta data nuna masa tsiraicin ta ba.
Bayan likitan ya gama duba lafiyar fatar matar sai ya shida mata cewa babu wata matsala a tare da fatar ta.
Karanta wannan labarin
Saurayi Yayi Silar Sakin Wata Amarya A Daren Farko Bayan Turawa Mijinta Hotunanta Na Lalata
Sannan kuma yacewa matar, fatar ki tana da kyau, amma matar sai ta kaiwa mijin ta korafi kan hakan inda tace likitan ya keta dokar musulinci, shafin hausaloaded ya ruwaito.
Daga nan mijin matar mai suna Azhimov mai shrkaru 29 ya bayyana cewa, ina da tabbacin likitan ya yaba da surar matar sa yayin da yake duba lafiyar ta, hakan bai dace da tsarinsa ba.
Idan kai likita ne kayi aikin ka kada ka zake da tambayoyi da yaba surar jama’a don wannan ba aikin likita bane.
Sai dai kuma likitan ya tabbatar da cewa, ya sanar da matar halin da fatar ta take ciki ne.
Karanta wannan labarin
Inda mijin matar ya shiga ofishin likitan sannan ya fara naushin sa akan hanci.