Advertisement

Atisayen da rindinar sojojin Nigeria ta gudanar Tasa Hankali ‘yan Bindiga da ‘yan Boko Haram Yamutukar tashi

Rundinara Sojojin Nigeria ta gudanar da wani atisaye na musamman a yau talata.

A Yammacin yau muka Sami rahotan rundinar Sojojin Nigeria sungudanar saban atisaye na musamman.

Babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya Janar Faruk Yahaya cikin sanarwar da rundunar sojin ta fitar ranar Talata ya ce an ƙaddamar da atisayen ne.

Domin magance ayyukan ta’addanci da garkuwa da mutane da fashi da makami da rikicin makiyaya da dukkanin ayyukan ɓarna a Najeriya.

Kuma sabon yunƙurin na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun ƙaruwar tashin hankali a yankin ƙabilar Igbo da ke kudu maso gabashi da matsalolin ƴan fashi da makami da hare-haren Boko Haram da Iswap a shiyyoyin kasar.

Manjo Shu’aib Umar, wanda ya yi magana a madadin babban daraktan hulda da jama’a na rundunar sojan ƙasa, Birgediya janar Onyema Nwachukwu, ya shaida wa BBC cewa za a gudanar da atisayen sojin ne lokaci guda a faɗin ƙasar.

Baya dahaka manjo shu’aib Umar ya bayyana garurunda za a gudanar da wannan saban atisayen.

Manjo Shu’aib Umar ya ce bayan atisayen Enugu, za a kuma yi atisayen a runduna ta biyu a Ibadan da runduna ta shida da ke Fatakwal da runduna ta 81 da ke Legas, da kuma yankunan ajiye bayanan sojojin kasa da runduna ta musamman ta 401 da kuma birget ta fadar shugaban ƙasa.

Kuma atisayen ya ƙunshi rundunonin da za su yi yaƙi da matsalolin tsaro a yankunan Najeriya guda huɗu.

To jama’a zamu so mukarbi ra’ayoyinku a sahinmu na tsokaci kada Kumanta Kuna tare Dani A.Usman Ahmad a shafinmu na Dalatopnews.

KU KARANTA WANNAN:

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama mutane 7 da ake zargin sun kashe babbab malamin addini

Bayan Hatsarin Motar Da Adam A Zango Da Ado Gwanja Sukayi A Niger Yanzu Sun iso Gida Lafiya

Subhanillahi Yadda Wasu Matasa Sukayi Abinda Bai Daceba A Ranar Yanci Kai Da Kai Da Ya Jawo Musu Martani Mai Zafi

Gaskiyar Lamari Akan Kama matar Gwamnan Kano Ganduje

Kada kumanta kudanna Mana alamar kararrawar sanarwa Domin samin Jin kararrawar shirye-shiryanmu masu kayatarwa mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button