Bayan Hatsarin Motar Da Adam A Zango Da Ado Gwanja Sukayi A Niger Yanzu Sun iso Gida Lafiya

Kamar Yadda Kuka Sani Dai A Yan Kwanakin Nan Ne Wani Mummunan Al’amari Ya Faru Ga Adam a Zango Da Mawaki Ado Gwanja A Hanyarsu Ta Zuwa Kasar Niger.
Abun Daya Faru Ga Wadannan Jarumai Guda Biyu Ba Komai Bane Face Wani Hatsari Da Sukayi Kuma Akayi Rashin Dace, Mutum Hudu Suka Mutu A Wannan Hatsarin.
Adam a Zango Da Mawaki Ado Gwanja Sunje Kasar Niger Ne Da Niyyar Yin Wasa Sai Wannan Mummunan Al’amari Ya Auku Akan Hanya.
Ku Karanta Labarin Nan:
Hatsarin Mota: Yanzu Adam A Zango Da Ado Gwanja Suka Tsallake Rijiya da Baya
Bayan Faruwar Wannan Al’amari Na Mutuwar Mutum Hudu A Hatsarin Da Su Ado Gwanja Sukayi, Sai Jita-jita Take Ta Yawo Akan Cewa An Rike Su Ado Gwanja Da Adam A Zango A Can Kasar Niger Din za’a Yanke Musu Hukunchi.
A Wani Guntun Video Da Jarumin Ya Wallafa A Shafinsa Na Instagram An Bayyana Cewa Lokacin Da Lamarin Ya Auku Ba Adam A Zango ne Ko Ado Gwanja Suke Jan Motar Ba Wani Ne Yake Jan Motar Hakan Ta Auku.
To Amma Dai Hausawa Sunce Biri Yayi Kama Da Mutum, Domin Kuwa Tun Lokacin Da Al’amarin Ya Auku, Bamuga Jaruman Sun Dawo Gida Nigeria Ba Sai Yau, Wanda Hakan Yakan Iya Daukansu Tsawon Sati Daya Da Aukuwar Lamarin.
Ga Wani Hoto Da Jarumi Adam a Zango Ya Wallafa A Shafinsa Na Instagram Tare Da Nuna Godiyarsa Ga Allah Akan Basu Dama Ta Fitowa Daga Cikin Kasar Niger, wanda Hakan Yana Nuna Anwakesu Daga Duk Wani Laifi Da Ake Zargi.
Toh Allah Ya Kara Kiyayewa Gaba, Daman Shi Dan Adam Baya Rabuwa Da Jarrabawa Ko Kaddara Idan Tazo Maka Babu Makawa Sai Abun Ya Auku Allah Yasa Mudace.
Zamu So Mu Karbi Ra’ayoyinku A Sashenmu Na Tsokaci Akan Wannan Al’amari Daya Faru Na Jaruman Nan Guda Biyu.
Sannan Munaso Ku Watsa Labarin Nan Domin Yaje Kunnen Masoya Wadanann Jaruman Domin Su San Halin Da Ake Ciki Yanzu.
Munaso Ku Danna Alamar Kararrawa Domin Samun Sababbin Shirye-shiryenmu Akoda Yaushe Mungode.
Ku Karanta Wannan Labarin:
Shin Da Gaskene Sai Anyi Lalata Da Yam Mata Kafin A Sakasu A Cikim Film
Sanadiyyar Lalacewa Rayuwar Yam Mata Biyu A Kannywood Sun Ishemu Darasi Cewar Sunusi Oscar 442
Tirkashi Yanzu Malam Yayi Kaca-kaca Da Masu Kallon Film Din LABARINA SEASON 3