Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama mutane 7 da ake zargin sun kashe babbab malamin addini

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayyana cewa ta kama mutum bawaki 7 wanda ake zargin su da sa hannu a kisan wani malami a jihar ta Kano.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ta Kano Abdullahi kiyawa, ya bayyana cewa mutanen sun ce suna zargun shugaban na CAN da boye wani mai laifi ne.
Rohoton yana nuna cewa faston mai suna Yahanna, ya jefa kansa a cikin al’amarin wani mutumi da mutane suke zarginsa daya hallaka matar ‘yayan sa.
Karanta wannan labarin
Shin Da Gaskene Sai Anyi Lalata Da Yam Mata Kafin A Sakasu A Cikim Film
Rundunar ‘yan sandan ta jihar Kano ta tabbatar da kame wasu mutane guda bakwai 7 dake da hannu a kisan shugaban kungiyar kiristoci na (CAN), na karamar hukumar sumaila dake jihar Kano, Shuibu Yahunna, kamar yadda shafin hausa legit suka ruwaito.
Mista Yahunna babban malamin addinin kirista ne wanda ya rasa rayuwarsa a hannun wasu mutane a kwanakin da suka gabata.
Sannan kuma shugabannin kungiyar kiristoci dake jihar Kano sunyi kira ga hukumonin jihar dasu tabbatar da adalci akan kisan da aka yiwa dan uwansu.
Karanta wannan labarin
Sanadiyyar Lalacewa Rayuwar Yam Mata Biyu A Kannywood Sun Ishemu Darasi Cewar Sunusi Oscar 442
Kamar yadda rahotanni suka tabbatar da cewa: al’amarin ya fara ne run ranar 22 ga watan satumba, a lokacin da wani mai suna Sabo Idris ya kashe matar yayan sa sakamakon wani sabani da suka samu.
Sai dai kuma faston mai suna Yahunna ya shiga cikin al’amarin inda mutane suka fara zarginsa da boye Sabo Idris, wanda ya canja addini sa zuwa addinin kirista.
Akan haka ne mutanen yankin suka hallaka faston mai suna Yahunna, sannan kuma suka kone cocin nasa da gida sannan da makarantar da yake jagorancin ta.
Kakakin ‘yan sandan jihar Kano Abdullahi kiyawa, a lokacin da yake shira da BBC Hausa a ranar litinin da tamma, ya bayyana cewa jami’an tsato sun danke mutane shida 6 a wajan da aka aikata kisan.
Karanta wannan labarin
A binciken da ‘yan sandan sukayi, wadanda ake zargin sun bayyana cewa, suna zargin faston da boye wani mutumi da yakashe matar yayan sa.
Sannan daga baya wani mutumi shima ya kawo kansa wanda yana cikin wadannan mutanan da suka aikata laifin, a halin yanzu mun kama mutane bakwai 7 wanda suke da hannu a kisan faston.
Wannan babban al’amari ne da bazai yiwu a kammala shi lokaci guda ba, muna bukatar hujja kuma yanzu haka mun kama hanyar bincike.