Sanadiyyar Lalacewa Rayuwar Yam Mata Biyu A Kannywood Sun Ishemu Darasi Cewar Sunusi Oscar 442

Babban Mai Bada Umarni A Kannywood Wato Sunusi Oscar 442 Ya Cillo Wata Magana Wanda Ta Zamto Cece Kuce A Kafafen Sada Zumunta.

Hakika Abubuwa Da Dama Sun Faru Acikin Masana’antar Kannywood, Wanda Suka Zama Izna Da Kuma Abun Fahimta Ga Duk Wani Mai ilimi Ko Hankali Acikin Masana’antar.

A Cikin Masana’antar Kannywood Anyi Jarumai Da Dama Masu Shahara Kuma Ababen Kwatance, Wanda Daga Baya Wasu Sun Mutu, Wasu Kuma Suna Nan Amma Sunbar Harkar Ko Doriyarsu Ba’aji.

Shiyasa Duk Wanda Ya Fahimchi Mecece Rayuwa Bazai Nayin Girman Kai Ko Jiji.Da Kai Ba, Domin Kuwa Wata Rana Ko Yana So Ko Bayaso Sai Kujerar Nan Ta Saukeshi Ta Kawo Masu Tasowa.

Domin Kuwa Acan Baya A Masana’antar Kannywood Anyi Jarumai Da Dama Masu Shahara Kamar Su Balaraba Muhammad, Aminu Garba, Ahmad S Nuhu, Hauwa Ali Dodo Wato Biba Probelm Da Dai Sauransu Wadanda Dukkansu Sun Bar Duniya Sun Koma Ga Allah.

Sannan Kuma Akwai Jarumai A Kannywood Yanzu Kamar Su Ummi Zeze, Fatima Muhammad, Fati Baffa Fage Wanda Suna Raye Amma Basa Fitowa Acikin Fina-finai.

To A Wannan Zamaninma Akwai Wasu Jarumai Da Rayuwarsu Ya Kamata Ta Zama Darasi A Masana’antar Kamar Yadda Mai Bayarda Umarni Sunusi Oscar Ya Wallafa A Shafinsa Na Instagram.

Darakatan Yayi Wannan Bayani Ne Wanda Hausawa Sukw Cewa Mai Kurman Baki, Domin Kuwa Bai Bayyana Matan Da Yake Nufi Ba.

Amma Dai Wasu Daga Cikin mabiya Darakatan Sunyi Ta Tofah Albarkachin Bakinsu Akan Wannan Al’amari Daya Faru Ga Kadan Daga Cikin Korafin Da Mutane Sukayi Tayi Akan Bayaninsa.

 

To Allah Ya Kyauta Zamu so Mu Karbi Ra’ayoyinku A Sashenmu Na Tsokaci Akan Wannan Bayani Na Sunusi Oscar 442.

Ku Karanta Wannan Labarin:

Mamallakin Manhajar Facebook Da Instagram Ya Nemi Gafarar Mutane Akan Abunda Ya Faru Jiya

Ku Karanta Wannan Labarin:

Tirkashi Shin Kunsan Dalilin Dayasa Facebook, Whatsapp Da Instagram Suka Tsaya Da Aiki?

 

Ku Karanta Wannan Labarin:

Wasu tsofaffin jaruman kannywood mata da auren su yayi albarka har ma suka cimma wani matsayi

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button