Wannan magana da Mai girma tsohon Gwamnan Jiahar Jigawa Alhaji Sule Lamido yayi Ta Janyo ce-ce kuce Akafafan yada labarai.

Baza mutaba bawa kudancin Nigeria takarar Shugaban kasa a shekara ta dubu biyu da a Shirin 2023.
A safiyar yaune muka Sami wani rahotan daga shafin BBC Wanda mukaci Karo two hon Gwamnan jiahar jigawa Alhaji Sule Lamido Yana wani tsokaci akan lamarin siyasar Nigeria.
Tsohon gwamnan ya ce ba laifi bane idan an yi hakan saboda tunanin zaman lafiya da kuma son farfado da tasirin jam’iyyar a yankin arewa, wadda ake sa ran za ta karbi mukamin shugabancin jam’iyyar.
Idan ma haka ta tabbata, sai dai a yi saboda zaman lafiya, misali akwai wadanda ke cewa yanzu PDP ba ta da karsashi a yankin arewa, don haka akwai bukatar a samu wani daga yankin da aka tabbatar da sahihancinsa a bashi shugabancin don farfado da tasirinta, to idan an yi haka ba lafi bane, amma idan aka ce dole sai dai a kai kudu, to wannan ba za ta yiwu ba inji shi.
Ya kara da cewa ”ai an taba yin haka a PDP, aka dauko Obasanjo aka ce shi kadai zai yi takara, amma ka ga ai ba dole aka yi wa mutane ba, an yi ne domin ci gaban kasa da kuma son tabbatar da zaman lafiya da karuwar arziki a Cikin wannan kasa tamu Baki Daya.
Da wannan muka kawo karshen ruhotan namu na safiyar yau zamu so mukarbi ra’ayoyinku akan wannan magana ta Mai girma Sule Lamido a sahinmu na tsokaci.
Ku kasan tare dani A.Usman Ahmad Domin Jin wani rahotan kada kumanta kudanna Mana alamar kararrawar sanarwa Domin samin Jin kararrawar shirye-shiryanmu masu kayatarwa mungode.
KU KARANTA WANNAN:
Tirkashi Shin Kunsan Dalilin Dayasa Facebook, Whatsapp Da Instagram Suka Tsaya Da Aiki?
Matar data fillewa mijinta Kai ta shiga Hannun ‘yansanda a kasar gana.
Yadda Masu Garkuwa Da Mutane Sukayi Mana Fyade Nida ‘Yata Da Mijina Saurari Labarin Wata Mata
Masha Allah Mota Ta Kashe Wanda Yayi Zanen Batanchi Ga Annabi Muhammad (SAW) A Kasar Sweden