An kama dalibai Mata masu Shirin tada zaune tsaye Wanda suka gudanar da zanga-zanga a jami’ar Maiduguri.

Tofa dalibai Mata na jami’ar Maiduguri sungudanar da zangazanga a Cikin makarantar Wanda Hakan ya jawo musu matsala.

Wani gajeran bidiyo ya nuna yadda jami’an tsaro suka kai samame dakunan ɗalibai mata na jami’ar Maiduguri inda suka kwashe mutum 38.

Jaridar BBC sun shaida cewa waɗanda aka cafke sun hada da matan da suka shiga zanga-zanga kan karin kudin makarantar da rayuwar wahala da suke yi a jami’ar.

Daruruwan dalibai mata ne suka yi zanga-zangar lumana domin nuna adawa da karin kudin makaranta, sai dai jami’an tsaro sun yi ta datse su.

Majiyoyi sun ce anyi ta amfani da karfi domin dakile daliban daga zanga-zangar.

An jikkata dalibai mata da dama a lokacin boren, yayinda aka rawaito cewa jami’an tsaro sun yi ta gallazawa wasu da dorina.

Wanda dukan da daliban da sukasha yawuce misali.

Akalla an cafke dalibai 18 kuma ana tsare da su a ofishin jami’an tsaron jami’ar cikin yanayi na akuba har zuwa wayewar garin Talata.

A lokacin mayarda martani Farfesa A. M. Gimba, da ke kula da harkokin ɗalibai ya ce ya yi gargadin cewa mahukunta makarantar za su dau matakai masu tsauri kan wadanda suka yi kokarin tada zaune tsaye a makarantar.

A yanzu haka daliban da suka shiga hannu su ake tuhuma Dan tabbatar da daliban da suka Fara hada wannan zanga-zangar limana din.

Ku cigaba da bibiyarmu a shafinmu na Dalatopnews Domin samin sabbin labaran Duniya.

Nine a harkullum A.Usman Ahmad  Dauke da Labaran Duniya.

KU KARANTA WANNAN:

Za a dinga biyan daliban da suke fannin koyarwa kudade a duk karshen zangon karatu Mai digiri (75,000) Mai NCE (50,000) wannan yakawo CeCe kuce ga daliban da suka Gama karutu musamman NCE a Kafar Sada zumunta.

Mansurah Isah Ta Aikata Abunda Hadiza Gabon Tayi A Kwanakin Baya

Kalli bidiyon jarumar kannywood Fati KK yadda take tikar rawa a TikTok

Yadda Wasu Fusatattun Matasa Sukayiwa Wata Yar Majalissa A Jihar Ruver Dukkan Tsiya

Wata mata mai juna biyu ta hada baki da mutane 2 domin suyi garkuwa da ita ta sami kudi a wajan mijinta

Wannan sune Abubuwan da auran kananan ‘Yan Mata yake janyowa.

Kada kumanta kudanna Mana alamar kararrawar sanarwa Domin samin Jin kararrawar shirye-shiryanmu masu kayatarwa mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button