Direban Motar Dayake Daukan Fasinjoji Yana Kaiwa Wajen Masu Garkuwa Da Mutane Asirinsa Ya Tonu Yanzu

Subahanallahi Wannan Mummunan Al’amari Dame Yayi Kama, Duk Da Kun Sani Dai A Yanzu Babu Abunda Yafi Tayar Da Hankalin Jama’a Sama Da Garkuwa Da Mutane Da Kuma Fashi A Arewachin Nigeria.

Kuma Kullum Abun Cigaba Yakw Karayi Ba Baya Ba, Amma Wasu Suna Tambayar Mai Yasa Gwamnati Bata Dauki Mataki Akan Wadannan Mutanen Ba.

To Abun Duba Anan Shine, idan Ya Zamto Zalunchin Da Akeyi Maka Akwai Wasu Hadin Bakin Wasu ko Kuma Goyon Bayan Wasu Mutanen Da Suka San Sirrinka Toh Zaka Sha Wahala Kafin Ka Gano Matsalar.

A Nan Kuma Mun Samu Wani Labari Na Wani Direba Dayake Daukan Fasinjoji Yana Tafiya Dasu, Sai Yazo Dai-dai Wajen Masu Garkuwa Da Mutane Sai Ya Tsaya Yace Motar Ta Lalace, Daga Bisani Masu Garkuwa Da Mutanen Su fito Su Kama Dukkan Mutanen Motar Har Dashi.

Sai Daga Baya Su Sakeshi, Su Kuma Sauran Mutanen A Rikesu Sannan A Nemi Kudin Fansa Ga Yadda Rohoton Yake.

Direban dake kai fasinja wajen yan
bindiga don a yi garkuwa da su ya shiga hannuRundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta
yi holan Hamisu Sule wani direba dake daukar fasinja
yana tsayawa da su a daidai wajen da ‘yan bindiga
suke fitowa domin suyi garkuwa da mutane.

A cewar kakakin rundunaryan sandan babban birnin
tarayya Abuja Frank Mba, shi wannan direba, bakinsa
daya da ‘yan bindigar dake sace mutane suna yin
garkuwa da su, idan ya dauko mutane sai yazo wajen
da ya san ‘yan bindigar na labe sai ya nuna mota tasamu matsala.

Daga bisani kuma sai ‘yan bindiga su fito daga daji su
yi awon gaba da mutane. Mba ya kara da cewar, sun
samu bayanan sirri akan direban dan haka suka danamasa tarko har suka kamo shi.Haka nan kuma Kakakin rundunar ya bukaci mutaneda su daina hawa mota a bakin hanya ba tare da sun
shiga tasha ba.

Toh Allah Ya Shiga Tsakanin Nagari Da Mugu Ameen.

Munaso Ku Danna Alamar Kararrawa Domin Samun Sababbin Shirye-shiryenmu Akoda Yaushe Mungode.

Ku Karanta Wannan Labarin:

Tirkashi Yanzu Magan Ta Fito Fili Akan Kama Matar Ganduje Da Hukumar EFCC Tayi

Atisayen da rindinar sojojin Nigeria ta gudanar Tasa Hankali ‘yan Bindiga da ‘yan Boko Haram Yamutukar tashi

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama mutane 7 da ake zargin sun kashe babbab malamin addini

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button