Subahanallah: Yadda ‘yan bindiga suka kai mummunan hari jihar Zamfara sunyi ta’asa

Miyagun ‘yan bindiga sun kai mummunan hari wani kauye dake kuryar madaro, karamar hukumar kauran Namoda a jihar Zamfara.

A rahoton da BBC Hausa da samo ya bayyana cewa, maharan ‘yan bindigan sun hallaka mutane da dama sannan kuma suka kone gidajen mutane tare da motocin su.

Wasu wanda sun kasance a yankin sun tabbatar da cewa, maharan ‘yan bindigan sun shiga kauyen ne da misalin karfe goma na dare, sannan sun dauki tsawon lokaci sun aikata abin da sukaga dama.

Haka kuma ‘yan bindigan sun debi kayan abinci a shagunan ‘yan kasuwa wanda suke zaune a yankin, har ma da dabbobin mutane.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta Zamfara ta tabbatar da kaiwa harin da ‘yan bindigar sukayi, amma sai ta bayyana cewa tuni aka tura jami’an tsaro domin sukai dauki wajan.

Wannan kauyen da maharan ‘yan bindigan suka kai hari yana daya daga cikin yankunan da hukuma tasa aka datse yin amfani sabis da kuma intanet.

Amma wasu mutane da sukayi nasarar tserewa daga yankin suka koma Gusau inda aka barsu suyi amfani da sabis sun bayyana cewa, maharan ‘yan bindigan sun kona gidaje 13 da motoci 16.

Kalli hotunan da maharan ‘yan bindigan suka kai hari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button