Wata mata mai juna biyu ta hada baki da mutane 2 domin suyi garkuwa da ita ta sami kudi a wajan mijinta

Wata mata mai suna Nafisa saleh ta hada kai da wasu mutane guda biyu 2 domin sunyi garkuwa da ita, al’amarin ya faru ne a Damaturu babban birnin jihar Yobe tun ranar daya 1 ga watan oktoba 2021, inda matar ta boye kanta yayin zuwa asibiti don tayi awu.
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, an nemi matar an rasa ta run ranar daya 1 ga watan oktoba 2021, a lokacin da ta tafi asibiti domin a mata awu na ciki.
Bayan anyi garkuwar da ita da wanda suka hada kai sai suka kira mijinta domin ya biya kudin fansa.
Karanta wannan labarin
Lallai Dole Auren Hausawa Ya Dinga Mutuwa, Musamman Arewachin Nigeria Kalli Videon Nan
Sai dai kuma a binciken da ‘yan sanda sukayi sun gano cewa, matar mai suna Nafisa Saleh da kanta tasa akayi garkuwa da ita domin ta sami kudi a hannun mijin nata.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Yobe, ASP Dungus Abdulkarim a wata takarda a ranar Talata ya bayyana cewa ‘yan sandan sunyi gaggawa ne wajan fara aikin inda suka gano gaskiyar lamarin.
A cewar Dungus ‘yan sandan sun kama mutane biyu 2, Goni Modu da kuma Umar mai Gudusu, wanda suke ‘yan kauyen Dadinge dake karamar hukumar Gujba jigar Yobe.
Karanta wannan labarin
Sai dai kuma anyi gaggawar kaiwa Nafisa Saleh asibiti domin duba lafiyarta sabida halin da aka tsinceta a ciki.
ASP Dungus Abdulkarim ya kara da cewa, sun kama wasu mutane 2 wanda ake zargin sunyi garkuwa wani yaro mai shekaru 3 a karamar hukumar potiskum dake jihar Yobe.
A cewar sa duk wadanda ake zargin yara ne, daya yana da shekaru 14 daya kuma 12 sannan kuma akwai na ukun wanda shi ya tsere.
Karanta wannan labarin
Gwamnan Kadunan El-Rufa’i Yasan Inda Yan Ta’adda Suke Buya Wani Dan Bindiga Yayi Bayani