‘Yan bindiga sun hallaka mutane goma sha tara 19 ciki har da kananan yara da mata sannan suka kone gidahe

Mutane goma sha tara 19 a kalla suka rasa rayukan su lokacin da maharan ‘yan bindiga suka kai hari kauyen kuryar Madaro dake jihar Zamfara.
Al’amarin ya faru ne a ranar Talata cikin wadanda suka rasa rayukan nasu har da kakanun yara, bayan wannan kuma ‘yan bindigar suka bankawa shaguna wuta.
Al’amarin ya auku ne yayin da kwamishinan ‘yan sandan jihar, Haruna Elkana ya kaiwa ‘yan sanda dake hanyar shinkafi zuwa kaura Namoda ziyara.
Karanta wannan labarin
Tirkashi Wata Budurwa Ta Fashe Da Kuka Tare da Nemi Gafarar Iyayenta Bayan Fitar Bidiyon iskanchinta
Kamar yadda jaridar Premium Time ta ruwaito yadda ‘yan bindigar suka kai farmakin a washegarin da kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ayuba Elkana, ya kaiwa wasu ‘yan sanda na musammam da suke aiki a hanyar shinkafi zuwa kaura Namoda ziyara.
Kauyen kuryar madora yana karkashin karamar hukumar kaura Namoda amma yana da iyaka a zurmi da kuma shinkafi, wajan da ta’addancin yafi yawai a jihar ta Zamfara.
Jaridar Premium Time ta ruwaito yadda wata majiya ta sanar da BBC Hausa cewa, maharan ‘yan bindigar sun kwasge sa’o’i da yawa a kauyen suna tafka ta’addanci.
Karanta wannan labarin
Wannan Shine Dalilin Dayasa Ma Auri Jarumar Kannywood Cewar Shu’aibu Lilisko
‘Yan bindigar sai da suka saci abubuwa da dama a shagunan mutane sannan suka saci dabbobin da mutane suke kiwatawa.
Haka kuma wata majiya ta daban, Mustapha mai leda ya tabbatarwa da Premium Time faruwa lamarin, kamar yadda yake cewa.
Mun binne mutane goma sha tara 19 wanda ‘yan bindiga suka hallaka, akwai mutane da dama a asibiti wanda suka raunana sannan cikin mutane da suka hallaka har da kananun yara da mata wanda suka kara tserewa yayin da ‘yan bindigar suka kai farmaki.
Karanta wannan labarin
Karan da ‘yan hakidar shi’a suka shigar ya jawomusu matsal tsalu masu Yawa Wanda.
Wata majiyar kuma tace, ‘yan bindigar sun bankawa gidaje goma sha uku 13 wuta da ababen hawa goma sha shida 16 cikin har da na ‘yan sanda.
Kakakin rundunar ‘yan sandan ya tabbatar da farmakin da ‘yan bindigar suka kai, sai dai kuma bai fadi wani bayani a kai ba.