An sami nasarar ceto matunae 180 a Jihar zamfara Wanda masu.

Rundunar ‘yan sanda jihar Zamfara ta sanar da ceto sama da mutum 180 wadanda ‘yan fashin daji suka sace a kauyukansu.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Mohammed Shehu, ya fitar, yace mutanen sun shafe makonni a hannun ‘yan fashin dajin.
An yi nasarar ceto mutanen ne bayan wani aikin nema da ceto da jami’an tsaro suka yi a dajin Tsibiri da ke karamar hukumar Maradun a jihar ta Zamfara.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan ya ce tuni aka mika mutanen hannun jami’an gwamnati domin kai su asibiti a duba lafiyarsu.
Kan haka BBC ta tuntubi kwamishinan yada labarai na jihar ta Zamfara Ibrahim Dosara don jin a irin halin da aka samu wadannan mutane da aka ceto.
Ibrahim Dosara, ya ce an same su cikin yanayi na galabaita sosai, domin da yawa daga cikinsu an same su da kuraje a jikinsu saboda cizon sauro da makamantansu.
Ya ce,” Wasu daga cikin mutanen kuma saboda wahalar da suka sha ko tafiya basa iya yi sai an rike su, sannan kuma mata sun fi maza yawa a cikin mutanen.
Kwamishinan yada labaran ya ce, baya ga mata akwai kuma kananan yara na goye duk a cikin mutanen da aka ceto.
Ibrahim Dosara, ya yi bayanin cewa an samu nasarar kubutar da wadannan mutanen ne saboda irin matsin lambar da ake yi wa ‘yan fashin dajin, saboda matakan da gwamnatin jihar ta dauka na kakkabe su.
Ya ce matsin lambar da suka fuskanta ce ya sa suka gudu suka bar mutanen har aka kai ga gano su a kubutar da su.
Kwamishinan ya ce, da zarar an kammala duba lafiyarsu za a kai su domin sada su da iyalansu.
KU KARANTA WANNAN:
Dole Mu Saka Soyayyar Annabi Muhammad (SAW) A Zuciyoyinmu Cewar Atiku Abubakar
Har Yanzu Akwai Harsashi A Jikina Da Matata Cewar Sheik Ibrahim El-Zakzaky
Wani mutumi ya mutu a lokacin da yake tsaka da lalata da ‘yan mata 2
Kada kumanta ku dannamana alamar kararrawar sanarwa Domin samin Jin kararrawar sanarwa shiryeshiryanmu masu kayatarwa mungode.