Advertisement

Kotun Mumbai dake india ta yankewa dan gidan Shah Rukh Khan jarumin Bollywood hukuncin zama a gidan yari

Aryan khan dan shakaru 23 aduniya shine babban dan gidan jarumin Bollywood Shar Rhuck khan, shahararran jarumi na masana’antar shirya fina-finai ta Bollywood a kasar India.

Wata kotu a mumbai dake kasar India ta yankewa dan gidan Shah Ruckh khan mai suna Aryan Khan, hukuncin zama a gidan yari a tsawon na tsaeon kwana goma sha hudu 14, kamar yadda WASHINGTON D.S ta ruwaito.

An yankewa Aryan Khan wannan hukuncin ne sabida an kama shi da miyagun kwayoyi tare da wasu mutane bakwai 7 a wajan wani shagali wanja suka shirya a cikin jirgin ruwa na alfarna.

Karanta wannan labarin

Wani mutumi ya mutu a lokacin da yake tsaka da lalata da ‘yan mata 2

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na A.P ya ya bayyana, A ranar asabar data gabata ne aka dan gidan Sharu Ruckh Khan din Aryan Khan tare da wasu mutane, a dai-dai lokacin da aka kai mamaya cikin jirgin runan dake gefen gabas tekun Mumbai.

An tsare Aryan khan din bisa tsarin shari’a wanda zai kasance a karkashin kulawar kotu, a maimakon hukumar da take kula da ayyukan gyaran hali.

Shah Rckh Khan wanda yake da shekara 55 yana daya daga cikin shahararrun jarumai na duniya wanda har ma ake kiransa da King of Bollywood, ma’ana sakin Bollywood.

Karanta wannan labarin

Jaruma Hadiza gabon ta soki jarumi Ali nuhu dalilin katsalandan da sukayiwa jaruman shirin Big Brother

Shah Rukh Khan ya kwashe tsawon shekaru talatin 30 yana wasan kwai-kwayo a Bollywood, inda ya fito a cikin fina-finai sama da dari da biyar 105.

Jarumin Bollywood din Shah Rukh Khan yana da masoya sama da Miliyan arba’in da biyu a shafin sa na Twitter, sannan kuma shine wanda ya mallaki kungiyar wasan kulki ta cricket da ake kira, Night Rider, da ake buga wasa a gasar kasan india premeir league, wanda gasar wasan ta cricket itace tafi armashi a duniya.

Karanta wannan labarin

Tirkashi An Kai Karan Hafsat idris Kotu Kan Cinye Kudin Aiki/Whitemoney Ya Cinye Gasar BBNaija

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button