Advertisement

innalillahi Yanzu Aka Tona Asirin Hadiza Gabon, Ashe Dama Haka Rayuwarta Take

A Wata Bidiyo Da Muka Samu Daga Shafin Jarumin Film Din Hausa Na Tiktok Wato Auwal Isah Ways Ya Tona Asirin Jaruma Hadiza Gabon Biyo Bayan Wani Abu Datayiwa Ali Nuhu Da Adam A Zango.

Idan Zaku Iya Tunawa A Satin Daya Gabata Ne Aka Tattauna Batun Cin Gasar Da Wani Mutumi Mai Suna White Money Yaci Naira Miliyan Casa’in.

Yadda Har Muka Ga Jaruman Kannywood Su Ali Nuhu, Adam a Zango Da Abba El Mustapha Sun Tayashi Murna Har Akayi Wasu Hotuna Gasu Kamar Haka.

Toh Bayan Hotunan Na Da Kuma Bidiyon Abun Sun Karade Kafafen Sada Zumunta Na Taya Murna Ga Wannan Mutum Akan Cin Nasarar Gasar BBnaija.

Sai Jaruma Hadiza Gabon Ta Wallafa Wani Tsokaci A Shafinta Na Instagram Wanda Yake Bayyana Cewa Yan Kannywood Basa Daga Mutane Masu Tasowa, Kuma Wanda Suka Taya Murnar Ma Bai Kula Dasu Ba Domin Bai Wallafa Hotunansu A Shafinsa Na Instagram Ko A Story Ba Ga Abunda Jarumar Ta Fada.

 

Duk Da Dai Jarumar Tana Da Kanshin Gaskiya Domin Kuwa Idan Ya Zamto Mutane Suka Ziyarceka Kuma Akayi Hotunan Ko Bidiyo Yana Da Kyau Ka Wallafa Shi A Shafinka Na Sada Zumunta Domin Mutane Su Gani Kuma Su San An Ziyarceka.

Toh Bamuga Mutumin Da Jaruman Kannywood Suka Ziyarceshi Ya Wallafa Ko Daya Daga Cikin Abunda Akayi Ba, Shiyasa Jaruma Hadiza Gabon Tayi Tsokaci Akan Haka.

Amma Sai Dai Maganar Ta Tayar Da Kura Yadda Wani Jarumi Auwal Isah Ways Ya Tona Mata Asiri, Sannan Ya Bayar Da Tarihin Rayuwarta Tun Daga Farkon Shigowarta Masana’antar Kannywood Zuwa Yanzu Ga Bidiyon A Kasa Sai Ku Kalla.

https://youtu.be/Gz8sRcQ9RB0

 

Zamu So Mu Karbi Ra’ayoyinku A Sashenmu Na Tsokaci Akan Wannan Al’amari Sannan Munaso Ku Danna Alamar Kararrawa Domin Samun Sababbin Shirye-shiryenmu Akoda Yaushe Mungode.

 

Ku Karanta Wannan Labarin:

Masha Allah: Yanzu yanzu muka sami labari shahararran mawaki Nura M Inuwa ya sami karuwar ‘yar mace

 

Ku Karanta Wannan Labarin:

Subhanillahi Yadda Rigima Ta Barke Auwal Isah Yayi Kaca Kaca Da Hadiza Gabon

 

Ku Karanta Wannan Labarin:

Inna lillahi wa inna ilaihrraji’un: Allah ya yiwa mahaifin jarumi kuma mawaki Baban chinedu rasuwa

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button