Kafin na fara shirin fina-finan hausa na kannywood sai da nayi sana’ar gwangwan da kuma karan mota, cewar jarumi Tijjani asase

Ficaccan jarumin masana’antar kannywood kuma darakta na shirin fim din, Adumiya, Tijjani abdullahi asase ya bayyana cewa, ya fara neman kudi ne da sana’ar gwan-gwan.

Sanna kuma jarumin ya kara fadin cewa, yayi sana’ar yaron karen mota kafin ya shiga masana’antar kannywood, inda jarumin ya bayyana hakan a shirar su da Freedom Radio.

Jarumi Tijjani Abdullahi asase yace, babban abin da yake burge shi a rayuwa shine yaga matashi ya rike sana’a komai kankantar ta, sannan mutum ya kasance mai gaskiya da kuma rikon amana.

Karanta wannan labarin

Yanzu Hadiza Gabon Ta Mayarwa Auwal Isah Martani Akan Zaginta Da Tona Mata Asiri Da Yayi

Jarumi Tijjani Abdullahi asase yana yawan fitowa a shirin fina-finan masana’antar kannywood sannan kuma yana taka rawar gani sosai, wanda yake fitowa a matsayin dan fashi da makami ko kuma gawurcaccan mai aikata munanan laifuka.

Tijjani asase ya kara da cewa, Babban abin da yake haifar da matsaloli masu tarin yawa a yanzu wanda har ake sace-sace da tsarewa mutum a kwace kayansa shine, rashin dogaro da kai da matasa suke fuskanta sannan kuma suna raina kanana sana’o’i.

Sannan kuma jarumi Tijjani asase yayi fata akan masana’antar kannywood da suci gaba da shirya fina-finai wanda zasu sauya rayuwar al’umma.

Karanta wannan labarin

Makiyana basa farin ciki dani akan na shiga shirin fin din India, cewar jaruma Rahama sadau

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button