Makiyana basa farin ciki dani akan na shiga shirin fin din India, cewar jaruma Rahama sadau

Jamar yadda kuka sani dai Rahama sadau ficacciyar jaruma a masana’antar shirya fina-finan hausa ta kannywood har ma da shirin kudancin Nageriya wato Nollywood.
Wanda a yanzu haka jaruma Rahama sadau tana taka mushimmiyar rawa a shirin da take fitowa ba kasar India mai suna Khuda Haafiz, inda jarumar take godiya ga Allah kan damar data samu wanda ta dade tana bukatar shiga cikin fina-finai wanda suka sharaha, da fifafftun wakoki da tallace-tallace ciki da wajan Nageriya.
A wani sako data wallafa a shafin ta na sada zumunta ta bayyana cewa, duk da an dakatar da ita ko kuma an koreta daga masana’antar kannywood to duk lokacin data shiga wata matsala Allah yana sa hakan ya zame mata alkairi.
Karanta wannan labarin
Furodusa Alhaji sheshi ya yiwa jaruma Hadiza gabon zazzafan martani tare da kawali
Kamar yadda hausadailytime ta ruwaito, jarumar tace wannan ne yasa ta kafa kungiya mai zaman kanta mai suna, Today’s Care, domin kula da mabukata da kuma godewa Allah daya daga likafarta sannan ya kareta daga abokan gaba, da wadan basa mata fatan alkairi ko san ganin cigaban ta a harkar wasan kwaikwaiyo.
Jaruma Rahama sadau ta kara da cewa, tun tuni ta zama shahararriyar tauraruwa ta kasa da kasa kuma ‘yar kasuwa dake cikin rufin asiri, don haka wannan baya nufin bazata koma kannywood taci gaba da wasan kwaikwayo ba.
Ta kara da cewa, zan koma cikin babban shiri kuma na zama babbar producer a zahiri, ina tunanin tunanin bude gidan cinema a Kaduna domin mutane suna zuwa hutawa tare da iyayan su a lokacin bukukuwa.
Karanta wannan labarin
Ashe Alhakin Matashin Daya Sha Guba Akan Maryam Yahaya A Shekarun Baya Shiyake Binta Yanzu
Rahama sadau tace, a duk lokacin dana yanke shawarar na shiga wasu ayyuka abin da nake fara tunani shine mahaliccina, ba wanda suke zagina cikin ayyukana ba iyayena suna raye tare da ‘yan uwana ako da yaushe suna yimin addu’a Allah ya kiyayeni daga abokan baga kuma gaskiya ne, addu’ar su ta zama katanga mai karfi a tsakanina da makiyana.
Ta kara da cewa, ako da yaushe ina samin nasara kan aikin dana zaba a wasan kwaikwayo, a yau in kasar India muna daukar wani sabon fim kuma ina matsayin babbar jaruma mai jagorantar fim din ina jin yaren india sosai wanda hakan karin wata dama ce a gare ni, a lokacin da nake birnin New York tare da wasu fitattun mawaka na riga dana shiga Nollywood, a yanzu sunan Rahama sadau ya shiga kundin Hall of Fame inda manyan mutane maza da mata ne kawai zasu shiga kundin.
Karanta wannan labarin
Lalle Akwai Abin Dubawa A Tattare Da Da Maryam Yahaya Domin Tabbas Itama Taga Ta Duniya