Daga yanzu babu wata adawa a tsakanina da gwamnatin jihar Kamo, cewar Mustapha Nabraska

Daga yanzu babu wata adawa a tsakanina da gwamnatin jihar Kamo, cewar Mustapha Nabraska

Jarumin masana’antar kannywood kuma wanda yake harkar siyasa a karkashin jam’iyyar P.D.P Mustapha nabraska, ya bayyana cewa babu adawa a tsakanin su da gwamnatin jihar Kano a yanzu, jarumin ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da sukayi da Freedom Radio.

Mustpha Nabraska ya kara da cewa, sasacin da sukayi da gwamnatin ba karamin cigaba suka samu ba a dan kankanin lokaci, amma hakan ba yana nufin yin siyasa bane sai dai alakar yin aiki kawai tare da mutunta juna.

Karanta wannan labarin

Mutumin Dayafi Kowa Tsayin Hanci A Duniya

Sannan jarumin yace, Gwamnatin baya a karamar asara ta janyowa masana’antar kannywood ba, domin da yawa daga cikin daraktotin kannywood sai da suka bar jihar Kano suka koma wasu jihohin domin suci gaba da gudanar da ayyukan su.

Mustapha Nabtaska ya kara fadin cewa, har kawo yamzu sun kara samin kalubale da dama amma tunda suka gano inda zaren yake suka fara samin sukin abin, sannan kuma a yanzu sun dai na bin wata doka ko tsari na shugabancin hukumar tace fina-finan hausa.

Sannan yace, sunayin abin da sukaga yafi dacewa domin baka nema yasa suke yiwa hukumar tace fina-finan karan tsaye, domin duk wata matsala da suke fuskanta tana da alaka da shugaban hukumar.

Karanta wannan labarin

Shahararrun jarumai mawaka mata na masana’antar kannywood wanda suke tashe a yanzu

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button