Hana Fulani kiwo Ba a dal cibane Yana Daya daga Cikin abin da suke kawo matsal-tsalo acikin kasa Wanda abaya
Hana Fulani kiwo Ba a dal cibane Yana Daya daga Cikin abin da suke kawo matsal-tsalo acikin kasa Wanda abaya shiyasa aka

Hana Fulani kiwo bashine mafitaba saidama yakara budemana wata January barnan.
A safiyar yaune mukasamu saban rahotan daga Daya daga Cikin manema labaranmu na Jihar Legos Wanda ya shaidamana cewa Gwamnatin Legos ta Hana kiwo a yankinta.
A baya-bayan nan dai wasu daga cikin gwamnonin jihohin kudancin kasar ciki har da jihar Lagos suka dauki matakin kawo karshen kiwon sake a jihohin su.
Yayin wata ziyara da BBC Hausa ta kai jihar ta Akwa Ibom, ta yi tozali da wani makiyaya da ya koro shanunsa, inda ya bayyana mana cewa su kam a rediyo kawai suka ji an hana kiwo, amma su suna ci gaba da sana’arsu babu wata matsala.
Makiyayayin ya ce ”Muna haduwa da sojoji da ‘yan sanda, amma babu wanda ya taba ce mana komai, mu yanzu bamu san halin da muke ciki ba, an ce an hana kiwo amma ga shi mu muna ci gaba da yi” inji shi.
Shi ma shugaban kungiyar masu sayar da shanu a jihar Alhaji Muhammad Mijinyawa, ya shaida wa BBC cewa dama can sun bukaci mahukunta su basu karin lokaci domin su kammala shiryawa kafin fara amfani da wannan doka.
Ya ce ”A hakikanin gaskiya kafin su yi wannan dokar sun gayyace mu, kuma mun je majalisar dokoki mun gabatar da namu jawabin, mu ba mu ce ba mu yarda ba, don baza mu ja da gwamnati ba, don haka sai muka bukaci ya zama akwai mambobinmu a cikin wadanda za su jagoranci aiwatar da wannan doka, sannan a bamu lokaci mu sayar da kayan da muke da shi a yanzu, a kuma kebe mu a wuri guda tunda ba cewa aka yi mu bar jihar ba” a cewarsa.
Ko da yake ya amince kan cewa wasu daga cikin makiyayan na bata musu suna, sai dai a cewarsa wannan ba dalili bane da za a yi wa dukkaninsu kudin goro a matsayin bata gari.
”Abubuwan da Fulani ke yi sun wuce gona da iri, amma mu a nan Akwa Ibom ba haka abin yake ba, domin makiyaya masu yawo da shanun ma basu da yawa a nan, don haka ba ma samun irin wadannan matsalolin” inji shi.
Sai dai wani jami’in gwamnatin jihar, da ya nemi mu sakaye sunansa ya shaida mana cewa gwamna bai ce uffan kan hakan ba, amma alamu sun nuna amincewa da hakan, tun da babu wani mataki da aka dauka kan wadanda suka ci gaba da kiwon ba tare da wata tsangwama daga jami’an tsaro ba.
Wannan batu na hana kiwon sake a kudu maso gabashi da kudu maso yammacin Najeriya dai na ci gaba da daukar hankali da janyo zazzafar muhawara musamman daga bangaren arewa.
Inda wasu ke ganin ana nuna wa Fulani kiyayya da kabilanci da kuma sanya siyasa a lamarin, yayin da wasu kuma ke kallon samun wasu fulanin bata gari cikin masu aikata muggan laifuka a Najeriya ya kara taka rawa wajen janyowa wadanda ba su ji ba, ba su gani ba inda ake musu kudin goro.
Kucigaba da bibiyarmu a shafinnamu na Dalatopnews Domin samin labaran Duniya.
KU KARANTA WANNAN:
Shahararrun jarumai mawaka mata na masana’antar kannywood wanda suke tashe a yanzu
Yadda Akayiwa Wata Dalibar Islamiyya Dukan Tsiya Saboda Ta Halarchi Wajen Party
Kada kumanta kudanna Mana alamar kararrawar sanarwa Domin samin Jin kararrawar shirye-shiryanmu masu kayatarwa mungode.
One Comment