SERAP kungiyace Dake yaki da cinhanci da rashawa tabukaci da Muhammad Buhari yarage wasu kudade har naira biliyan 26 a Cikin kasafin kudin da yayi saboda aikin dazaiyi dakudin baida muhimmanci
SERAP kungiyace Dake yaki da cinhanci da rashawa tabukaci da Muhammad Buhari yarage wasu kudade har naira biliyan 26 a Cikin kasafin kudin da yayi saboda aikin dazaiyi dakudin baida muhimmanci

Ƙungiyar SERAP mai fafutukar yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ta buƙaci Shugaba Muhammadu Buhari da ya zaftare naira biliyan 26 daga cikin kasafin kuɗin kasar na shekara ta 2022.
A ranar alkamis 7 gawatan oktoba da misalin 12:40pm Shugaban kasar Nigeria Muhammad Buhari ya aiwatar da kasafin kude na karshan shekara 2022.
Kudaden wanda gwamantinsa ta ware ne domin wasu ayyuka da ƙungiyar take gani ba su da muhimmanci sosai idan aka yi la’akari da cewa gwamnatin za ta ciyo ba shine domin rage giɓin kasafin kuɗin.
A yayin gabatar da kasafin kuɗin da shugaban ya yi a gaban Majalisar Dokokin Ƙasar a ranar Alhamis 7 ga watan nan na Oktoba, ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta kashe wannan naira biliyan 26 wurin gina ɓangaren kula da lafiya na shugaban ƙasa, da tafiye-tafiye na cikin gida da na waje, da harkar abinci da liyafa, da alawus na zaman taro tare da na walwala da jin daɗi.
Ganin cewa ƙasar tana ta ciyo bashi ya sa ƙungiyar ta SERAP, a wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar 9 ga watan Oktoba ta nemi shugaban na Najeriya da ya yanke wannan kuɗi domin rage yawan bashin da ƙasar za ta ci wajen rage giɓin kasafin kuɗin.
Kuma gwamnatin ta yi amfani da wasu daga cikin kuɗaɗen da za a samu daga yankewar wajen inganta asibitoci da cibiyoyin kula da lafiya a faɗin ƙasar.
A dangane da hakan ne ƙungiyar ta buƙaci Shugaba Buharin da ya aika wa da Majalisar Dokokin Ƙasar ƙwarya-ƙwaryan kasafin kuɗi na wannan ragi da ta ce ya kamata ya yi domin samun amincewar Majalisar.
To jama’a zamu so mukarbi ra’ayoyinku akan wannan lamarin na kasafin kude na karshan wannan shekara 2022.
Haryanzu de kunatare Dani A.Usman Ahmad a shafinmu na Dalatopnews kucigaba da bibiyarmu Domin samin labaran Duniya kaitsaye.
KU KARANTA WANNAN:
Daga yanzu babu wata adawa a tsakanina da gwamnatin jihar Kamo, cewar Mustapha Nabraska
Sabida Matsalar Tsaro A Kasa Nigeria A Kalla Mutane 41Suka Rasa ransu A Makon da yagabata.
Kada kumanta kudanna Mana alamar kararrawar sanarwa Domin samin Jin kararrawar shirye-shiryanmu masu kayatarwa mungode.