Sheikh Aminu daurawa ya bayyana cewa babu maulidin Annabi Muhammad S.A.W a cikin koyarwar addinin musulinci

Sheikh Aminu daurawa ya bayyana cewa babu maulidin Annabi Muhammad S.A.W a cikin koyarwar addinin musulinci

A dai dai lokacin da muke cikin watan haihuwar Annabi Muhammad S.A.W wata tsohuwar bidiyon Sheikh Aminu daurawa take yawo inda malam Aminu daurawa yake amsan tambayoyin wani mutumi da yake tambayar sa kan cewa.

Malam akwai wani sako da yake yawo a Whatapp sai na rubuta shi da turanci nace Happy Birthday to you Rasulullah, kuma ance idan bamu ce komai ba bama son Annabi Muhammad S.A.W.

Sai malam Aminu daurawa ya bashi amsa da cewa, ana so a saka kayi maulid ne kaga kuma shi maulid babu shi a cikin koyarwar Annabi Muhammad S.A.W, baya cikin koyarwar sahabbai, baya cikin koyarwar su imamu malik kuma baya cikin koyarwar imamu shafi’i.

Malamin yaci gaba da bashi amsa tare da kawowa littatafai kala-kala domin ya nuna hujjar sa na rashin inganta maulid a cikin addinin musulinci.

Danna wannan link din na kasa domin ka kalli bidiyon.

https://www.hausaloaded.com/2021/10/maulidin-annabi-muhammadu-saw-babu-shi-a-cikin-koyarwar-addinin-islama-cewar-sheikh-daurawa.html

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button