Advertisement

Yanzu-Yanzu: Jaruma Hadiza gabon tasa an kama Auwal isah west dalilin wulakancin daya mata

Yanzu-Yanzu: Jaruma Hadiza gabon tasa an kama Auwal isah west dalilin wulakancin daya mata

A yau ne muka sami wani labari daga shafin sada zumunta instagram na Maufeeda Rasheed kan hatsaniyar dake tsakanin jaruma Hadiza gabon da Auwal isah west, inda tace tuni jaruma Hadiza gabon tasa aka kama Auwal isah west dalilin ya yi mata wannan cin mutuncin da wulakanci.

Kamar yadda wasunku suka sani jaruma Hadiza gabon tayi wasu rubuce-rubuce tare da maganganu akan jaruman masana’antar kannywood, kan cewa sunyi shishigi wajan shigewa jarumin Big Brother mai suna White Money inda suka dauki hotuna dashi, sai jaruma Hadiza gabon tace da sune bazasu yi musu haka ba.

Karanta wannan labarin.

Tirkashi Ansake Tona Asirin Hadiza Gabon/Abunda Rahama Sadau Take Shiyasa Ake Korarta A Kannywood

Jaruma Hadiza gabon ta kara da cewa: ko a story jaruman Big Brother din basu saka hotunan jaruman kannywood din ba balle ma suyi musu repost kodan asan sunayi, wanda wannan magana da jaruma Hadiza gabon tayi sai wasu suka dauke ta matsayin rashin kunya ga nagaba da ita kasancewar akwai manya kuma jiga-jigai na masana’antar kannywood a cikin wadanda suka halarci wajan taron da aka shirya irin su, Ali nuhu, Adam a zango, Baba karami, Abba el-mustapha.

Dalilin hakan yasa furodusa Alhaji sheshe da jarumi Auwal isah west suka yiwa jaruma Hadiza gabon martani, sai dai kuma a martanin da Auwal isah west yayi ya kama sunan jaruma Hadiza gabon inda yake martanin nasa da zagi da cin mutunci.

Kowa ya dauki wannan maganar ta wuce ashe jaruma Hadiza gabon bata kasar Nageriya tana Birnin Cairo, aiko nan take jarumar ta dauki haramar dawowa sai gata ta sauka a jihar Kano kamar yadda Mufeeda Rasheed ta bayyana, tun karfe biyu na ranar Hadiza gabon tasa aka aka nemo mata Auwal isah west sannan kuma aka tsare shi a hannun jami’an tsaro.

Karanta wannan labarin.

Kyawawan Hotunan Da Najlat Muhd Tayi Na Bayan Aurenta Da Dan Kwallon Nijeriya Shehu Musa

A yanzu haka Auwal isah west yana hannun hukuma yayin da ita kuma jaruma Hadiza gabon ta rufe wayarta kiran kowa ya daina shiga balle a sami damar da za’a bata hakuri tasa a sake shi ko kuma a sasanta maganar.

Karanta wannan labarin.

Kalli Bidiyon Beelalgy A Wajen Horon Yansanda Yana Kuka

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button