Advertisement
Trending

Yawan Cin Jan Nama Ya Saka Halitta Ta Zama Haka

Yawan Cin Jan Nama Ya Saka Halitta Ta Zama Haka

Tirkashi Kamar Yadda Kuka Sani Burin Yawanchin Da Adam Idan Ya Samu Walwala Ko Jin Dadi Bashi Da Buri Dayawa Wuce Yaga Abinchinsa Nama Ne Walau Na Kaza,Zabuwa Ko Naman Saniya Da Dai Sauransu.

Baya Da Haka Duk Abunda Kuka Sani Na Duniya A Nau’in Abinchi Yawaitarsa Yakan Iya Haifarwa Da Mutum Matsala.

Anan Kuma Sai Muka Tashi Da Wani Sabon Labari Akan Wani Ma’aikaci Gwamnati Mai Suna souleyman sy Wanda Sanadiyyar Cin Jan Nama Hannunsa Suka Zama Haka.

Kamar Yadda muka Samu Labarin Daga Shafin BBC Hausa, Rohoton Nasu Ya Fara Ne Kamar Haka;

Mutumin na fama ne da ciwon gaɓɓai na gout – wanda cin jan nama ke haifarwa. Cuta ce da ke samar da sinadarin uric mai yawa a jinin ɗan Adam, kuma yana faruwa ne sakamakon ruɓewar sinadarai a jikin mutum da ake kira purine da Ingilishi.

Akan samu purine a cikin abincin dabbobi da kuma saiwar tsirrai. Kazalika, an fi samun sa a cikin jan nama da kifi samfurin sadin da ababen maye da lemuka masu zaƙi da sauransu.

Yakamata mu Kula Da Cin Jan Nama, Abune Mai Hatsari.

Shi dai Souleymane ba wani abu ne ya saka shi cikin matsala ba illa jan nama.
Ina yawan cin jan nama a lokacin. Idan na samu lokacin hutu a wajen aiki, kodayaushe za mu tafi wurin mai nama mu ci kusan kilo daya. Ka ga kuwa muna diban nama da yawa. Na ci nama mai yawa kuma ina fama da sakamakon hakan,” a cewar Souleymane Sy.

Wani lokaci Souleymane kan yi nadamar cin nama mai yawa. Sai dai ba abu ne mai sauki ba mutum ya kauce wa cin nama a Kasarsa ta Jamhuriyar Nijar. Nama muhimmin Bangare ne na abincin yau da kullum a kasar.

Lokacin da yake matashin ma’aikacin gwamnati, Souleymane bai taka wuce tayi ba idan ya ga kilishi. Shi ma kilishi shahararren abin kwalama ne a Nijar.

Sinadarin purine da ake samu a abincin dabbobi ba shi kadai ne mafi hadari ba wajen kamuwa da ciwon gabbai na gout ba.

A cewar wani likitan koda a Nijar, Dr Alassane Amadou Seydou: “Akwai hanyoyi da ake iya kamuwa da wasu cutuka masu alaka da jini, kamar kansar jini kuma jinyarsu kan kai ga harbuwa da ciwon gout.

Sauran hanyoyin na da alaka da shan wasu kwayoyi kamar wadanda ake bai wa masu fama da tarin fuka ko ciwon zuciya.”

Ciwon Souleymane ya ta’azzara ta yadda aka samu wasu tsokoki sun tsiro a gabbansa, abin da ya haddasa masa rashin jin dadi. Bayan rashin barci da yake fama da shi da dare, kazalika yana shan wahala wajen yawatawa.

Hakan ya jawo gabbansa suka kumbura, abin da ake kira tophi, musamman a gwiwar hannunsa.

Sukan haddasa radadi a cikin kashi. Zugi da radadin kan faru ne cikin dare musamman a tafin kafa.

A cewar Farfesa Abdou Niang: “Zafin yana da tsanani sosai ta yadda mutum ba zai so ko takarda ta taba shi ba.”

Ciwon gabbai na gout ya fi shafar maza manya. Sai dai su ma mata kan kamu da shi.

Ba a fiya gane alamun ciwon gout ba saboda radadinsa yana da tsanani sosai.

“Duk sanda mutum ya kamu da ciwon gout ba zai taba mantawa da radadinsa ba,” in ji Farfesa Niang.

Haka nan, ciwon kan shafi musamman gwiwa, abin da kan jawo likita ya bukaci a maras lafiyar ya dauki hoton wurin domin gano matsalar.

Acikin Bayaninsa Yace; Sai Daya Siyar Da Kusan Komai Nasa Domim Magani

Ciwon ya shafi tattalin arzikin Souleymane. Ya sayar da kadarorinsa wajen jinya saboda ba shi da inshorar lafiya.

“Saboda neman lafiya, dole na sayar da wasu kadarorina…na sayar da motata da gidana. Saboda ina da wani gidan, shi ma na sayar da shi. Duk da haka har yanzu babu wani cigaba,” in ji shi. Amma ya ci alwashin Karar da duk abin da ya mallaka don ganin bayan ciwon da ya hana rayuwarsa sakat.

Ya yi kokarin bin umarnin da likitansa yake ba shi, wanda ya ce ciwon bai fi karfin magani ba.

“Ciwo ne da ake iya warkewa amma irin nasa dole ne mutum ya mayar da hankali kan nau’in abincin da yake ci a lokaci-lokaci,” a cewar Dr Seydou.

“Muna bai wa masu ciwon gout shawarar cewa su guji cin nama. Idan muna magana kan jan nama har kilishi ma yana ciki. Haka ma wake da kabeji, duka don a guji kara yawan sinadarin uric a cikin jiki. Muna bayar da shawarar mutum ya dinga cin kayan hatsi da kuma na marmari.”

Toh Allah Ya Kiyaye, Kuma Allah Ya Kara Kiyayewa Ameen.

Zamu So Mu Watsa Labarin Nan Domin Yaje Kunnen mutane Dayawa Domin Su San illar Da Jan Nama Yakeyiwa jikin Dan Adam.

Ku Karanta Wannan Labarin:

Mutumin Dayafi Kowa Tsayin Hanci A Duniya

Hana Fulani kiwo Ba a dal cibane Yana Daya daga Cikin abin da suke kawo matsal-tsalo acikin kasa Wanda abaya

Dole Nigeria sai ta Dauki shekara biyu ko uku tana Gyaran yadda Zasu gudanar da rugakafin maganin maleriya kafin a Basu (RTS,S) inji (UNICEF).

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button