Mu’azu magaji dan sarauniya ya yiwa Gwamna Ganjude martani da cewa birki ya kwace masa dalilin ya cire shi daga matsayin sa
Mu'azu magaji dan sarauniya ya yiwa Gwamna Ganjude martani da cewa birki ya kwace masa dalilin ya cire shi daga matsayin sa

Injiniya Mu’azu magaji dan sarauniya wanda tsohon shugaban kwamatin jawo iskar gas ne izuwa jihar Kano, yayiwa Gamnan jigar Kano martani dalilin tsige shi da akayi.
A cikin wani sakonni daya fitar a daren ranar Litinin ta cikin shafinsa na kafar Facebook, Mu’azu magaji dan sarauniya ya bayyana cewa birki ya tsinkewa Gwamnan Kano Abdullahi umar ganduje, kamar yadda Freedom Radio ta ruwaito.
Sannan ya kara da cewa dama zaman tare ne da HE AU yasa muke kokarin ceto jamiyyar mu APC tunda birki ya tsinkewa baba ganduje, don haka yanzu sai mu kauce sabida kar jini ya bata mana fararen kayan mu.
Sannan kima ajira matsayin mu a siyasa, amma bata tsiya-tsiya ba, duk masu yin tafiyar mu ta Win-Win Kano sabuwa amma hancin su a toshe sabida zama tare da mushe a daki daya to Alhamdu lillah.
Allah ya fito damu daga bakin…, yanzu zamu shaki iskar yanci kuma muyi siyasar yanci tare da kwatowa kanawa yanzi.
Daga nan ne mabiyansa suka fara yin tsaokaci tare da bayyana ra’ayoyin su kan wannan wallafar da yayi, haka kuma a nasa bangaren abokin tsamar sa a dandalin Facebook dan jarida Ja’afar Ja’afar har wata sabuwar bidiyo ya fitar a daren inda ya jajantawa Mu”azu magaji dan sarauniya sabida cire shi da aka yi daga wannan matsayin nasa.
Karanta wannan labarin.
Magana ta zama babba: Sadiya haruna tasa baki kan rigimar jaruma Hadiza gabon da Auwal isah west
Karanta wannan labarin.
Bayan Auwal Isah Ya Tona Asirin Hadiza Gabon Yanzu Sadiya Haruna Ta Shiga Rigimar
Karanta wannan labarin.
One Comment