Na daina saka sabbin jarumai mata a shirin fim dina kwanda suyi wata sana’ar ko suyi aure, cewar Abubakar bashir mai shadda
Na daina saka sabbin jarumai mata a shirin fim dina kwanda suyi wata sana'ar ko suyi aure, cewar Abubakar bashir mai shadda

Kamar yadda kuka sani Abubakar bashir mai shadda Darakta ne a masana’antar shirya fina-finan hausa ta kannywood, inda yake bayyana cewa ya dai na shigar da sabbin jarumai a cikin shirin fina-finan sa.
Darakta Abubakar bashir mai shadda ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a shirar da yayi da Freedom Radio, inda yake cewa, da yawa daga cikin sabbin jaruman da ake sanya su a cikin shirin fina-finai suna shiga ne ba tare da sanin iyayansu ba daga baya kuma sai su koma fitsararru a idan duniya.
Abubakar mai shadda ya kara da cewa: Ana samin kiran waya sama da hamsin ga ‘yan matan da suke bukata ya sanya su shirin fina-finan sa, sabida hakane ma yake basu shawara da cewa su koma makaranta domin neman ilimi idan kuma hakan ya gagare su sai su nemi miji suyi aure.
Bai tsaya nana ba ya kara da cewa: Su kan su jaruman da suka rage a masana’antar shirya fina-finan ta kannywood, yana musu fatan Allah ya kawo musu mazajen aure na gari domin su sami damar raya sunnar ma’aiki.
Mai shadda ya kara da cewa: Abubuwan sunyi yawa a masana’antar kannywood kamata yayi jaruman suna yin wasu sana’o’in ba harkar fim ba, don haka hakkin iyayansu ne su sanya ido akan ‘yayan nasu domin su hanasu fadawa cikin hali marar kyau.
Da aka tambayi Abubakar mai shadda cewa: Mai yasa mazan da ake shirin fina-finan dasu basa aurar ‘yan matan fim din sai Abubakar mai shadda yace, ai dukkan su suna da aure da matan su sannan kuma kowa yana da dalilin da yasa bazai auri ‘yar fim ba kuma wasu ma suna da mata hudu 4 don haka babu halin yin kari.
A wannan lokacin da ake kan tsaka da shirin fina-finai masu dogon zango ana yawan samin sabbin jarumai a harkar fim din.
Karanta wannan labarin.
Yadda Akayi Birthday Din Halima Buhari Babbar Yar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari
Karanta wannan labarin.
Karanta wanna labarin.
Kalli adadin yawan ‘yayan jaruman kannywood mata wanda ba kowa ne ya sansu ba
2 Comments