NDLEA tayi Nasarar Kama Mutane 134 a Jihar jigawa cikinsu harda.
NDLEA tayi Nasarar Kama Mutane 134 a Jihar jigawa cikinsu harda

NDLEA Sunyi Nasarar Kama wasu Yan kwaya dakuma har kimanin su dari da talatin da his 134 da wasu daliban makarantar.
A Yammacin yaune mukasamu saban rahotan daga Daya daga Cikin manema labaranmu na Jihar jigawa Wanda ke zaune a Hadejia yatabbatar Mana dakama ‘yan shaye shaye acikin Jihar.
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa NDLEA reshen Jihar Jigawa ta ce tayi nasarar kama mutane 134 bisa kamu su da laifin yin hulda da kwayoyi wanda kudaden su ya kai Miliyoyin Nairori cikin makonni 2 da suka gabata.
Da take gabatar da masu laifin da aka kama ga manema labarai Kwamandan hukumar ta Jihar Jigawa Malama Maryam Gambo Sani, ta ce an kama mutanen ne, biyo bayan sumamen da suka gudanar a ranakun 27 ga watan Satumba zuwa 10 ga watan Octoba.
A cewarta, a lokacin sumamen sunyi nasarar gano mashayar mutanen da dama.
Haka kuma ta ce kaso 99 cikin 100 na mutanen da ake zargin, suna amfani da kwayoyi ne, kuma suna cigaba da bawa hukumar bayanan sirri kan mutanen da suke sayar musu da kwayoyin.
Hajiya Maryam Gambo, ta ce daga cikin wadanda suka kama, 132 Maza ne, sai kuma 2 Mata, da wasu 2 masu sarautun gargajiya, tare da Ma’aikatan gwamnati 2.
Kazalika, ta ce sun yi nasarar kama Daliban Makarantun gaba da sikandire su 25 na Jihar nan a lokacin kamen.
To jama’a zamu so mukarbi ra’ayoyinku akan wannan lamarin Domin kawo gyara a Cikin sosayiti dinmu .
KU KARANTA WANNAN:
Yadda Akayi Birthday Din Halima Buhari Babbar Yar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari
Kashi 50% Cikin 100% Mata a Nigeria Basa amfani da internet Wanda wannan ya kawo.
Ya Kashe Makudan Kudade Saboda Halittarsa Ta Zama Kamar Ta Dabba
Kada kumanta kudanna Mana alamar kararrawar sanarwa Domin samin Jin kararrawar shirye-shiryanmu masu kayatarwa mungode.
One Comment