Subhanillahi Yadda Hadiza Gabon Tasa Aka Kama Auwal West Bayan Yayi Mata Tonon Silili Tare Da Gunduma Mata Zagi
Subhanillahi Yadda Hadiza Gabon Tasa Aka Kama Auwal West Bayan Yayi Mata Tonon Silili Tare Da Gunduma Mata Zagi

A Yammacin Jiya Litine Muka Sami Labari Daga Shafin Instagram Na Mufeeda Rasheed A Dandalin Instagram Kan Hatsaniyyar Da Ke Tsakanin Auwal West Da Hadiza Gabon Inda Ta Bayyana Cewa Tuni Jarumar Tasa Anyi Ram Da Jarumin Da Yayi Mata Zagin Tsamar Nama Wato Auwal West
Kamar Yadda Kuka Sani Hadiza Gabon Tayi wasu Rubuce Rubuce Da Maganganu Kan Jaruman Kannywood Da Cewar Sunyi Shishshigi Wajen Shigewa Jarumin Big White Money Suna Hotuna Dashi A Cewar Ta Da Nasu Ne Bazasu Yi Musu Haka Ba
Hadiza Gabon Ta Kara Da Cewa Ko A Story Jaruman Big Brother Din Basu Saka Su Ba Balle Suyi Musu Repost Balle Asan Suna Yi Wanda Wannan Magana Wasu Suka Dauketa A Matsayin Rashin Kunya Ga Nagaba Kasancewarsu Manya Jiga Jiga Masana’antar Kannywood Suka Halirchi Wajen Da Suka Hada Da Ali Nuhu, Baba Karamin,Adam A Zango,Abba El Mustafa Da Dai Sauransu
Hakan Yasa Producer Alhaji Shehi Da Auwal West Suka Yiwa Jarumar Raddi Sai dai Shi Auwal West A Nasa Raddin Ya Kama Suna Hadizan Ya Kuma Rufe Raddin Nasa Da Zagi Na Tsamar Nama Ga Wayanda Yace Yaran Da Suke Yiwa Manya Rashin Kunya A Social Media
Saide Kowa Ya Dau Maganar Ta Wuce Ashe Hadiza Bata Kasarnan Ne Tana Birnin Cairo Aiko Take Ta Dau Haramar Dawowa Sai Gata A Ranar Lahadi Ta Dira A Garin Kano Inda Kamar Yadda Mufeeda Ta Bayyana Misalin Karfe Biyar Na Ranar Tasa Aka Nemo Mata Shi Aka Kuma Tsareshi A Hannu Jami’an Tsaro
A Yanzu Haka Maganar Da Akeyi Auwal West Na Hannu Hukuma Yayin Da Ita Kuma Hadiza Gabon Ta Kashe Wayarta ,Kiran Duniya Ba’a Samunta Balle A Bata Hakuri Tasa A Sakeshi Ko Sasantawa Kamar Yadda Mufeeda Rasheed Ta Bayyana Wannan Lamari De Ya Zama Babba Muna Fatan Allah Ya Tsaida Wannan Rigimar Duk Da Cewa Duk Tsuntsun Da Ya Jawo Suwa Shi Ruwa Kan Duka.
Ku Kara Karanta Wannan Labarin
Tirkashi Ansake Tona Asirin Hadiza Gabon/Abunda Rahama Sadau Take Shiyasa Ake Korarta A Kannywood
Kyawawan Hotunan Da Najlat Muhd Tayi Na Bayan Aurenta Da Dan Kwallon Nijeriya Shehu Musa
3 Comments