Yanzu-Yanzu: Auwal isah west ya bawa jaruma Hadiza gabon hakuri akan wulakanci da tonon asirin daya mata
Yanzu-Yanzu: Auwal isah west ya bawa jaruma Hadiza gabon hakuri akan wulakanci da tonon asirin daya mata

A jiya ne jaruma Hadiza gabon tasa aka kama Auwal isah west kan walakanci da munanan magangaun da ya mata, inda har jarumar ta fusata tasa aka garkame shi.
Auwal isah west shima jarumi ne a masana’antar shirya fina-finan hausa ta kannywood wanda ba kowane ya san shi ba, sai a kwana biyu 2 da suka gabata Auwal isah west ya bayyana a cikin wata bidiyo inda yake wulakanta jaruma Hadiza gabon akan tayi martani ga wasu jaruman kannywood.
A cikin jaruman da Hadiza gabon tayi musu wannan martanin babu Auwal isah west amma haka kawai wallafa bidiyo yake tona mata asiri yake wulakanta ta, haka yaci gaba da zaginta hat sai da wasu mutanen suka fara jin haushin sa sabida bashi da hujja akan wannan chin mutunci da yake mata.
Sannan ko su jaruman da Hadiza gabon tayi musu martanin basu dauki wani mataki ba sukayi shiru da bakin su domin gudun kar wata hatsaniya ta faru a masana’antar ta kannywood.
Amma daga baya da jaruma Hadiza gabon tasa aka kama Auwal isah west sai gaba daya yayi sanyi har ma ake bukata ayi magana da jarumar domin tayi hakuri tasa a sake shi, sabida idan ya jima a wajan hukuma abin bazai yi dadi ba.
Sai a yanzu kuma jarumi Auwal isah west ya wallafa wata bidiyo a shafinsa na sada zumunta instagram yana mai bawa jaruma Hadiza gabon hakuri akan wannan wulakancin daya mata, kamar yadda zakuji daga bakin sa a cikin bidiyon.
Ga bidiyon nan domin ku kalla kuji yadda Auwal isah west yake bawa jaruma Hadiza gabon hakuri yana mai kaiwa goshin sa kasa.
Karanta wannan labarin.
Ya Kashe Makudan Kudade Saboda Halittarsa Ta Zama Kamar Ta Dabba
Karanta wannan labarin.
Karaanta wannan labarin.
Kalli adadin yawan ‘yayan jaruman kannywood mata wanda ba kowa ne ya sansu ba
2 Comments