An Karyata Sakon Da Ake Turawa Na Rufewa Whatsapp Din Mutane
An Karyata Sakon Da Ake Turawa Na Rufewa Whatsapp Din Mutane

Idan Baku Manta Ba A Jiya Mafiya Yawan Masu Amfani Da Kafar Sadarwa Ta Manhajar Whatsapp A Nigeria Da Saudiyya Zasu Ga Ana Tura Wani Sakon Murya,Yadda Aciki Ake Bayyana Duk Wanda Bai Turawa Wani Ba Za’a Rufe Masa Whatsapp Dinsa.
Bayan Ganin Abun Ya Farayin Yawa Yasa Muka Fara Bincike Akan Al’amarin Daga Baya Muka Samu Wani Cikakken Bayani Daga Shafin Twitter Na Daya Daga Cikin Ma’aikatan Manhajar Ta Whatsapp.
Daraktan Kamfanin Whatsapp varun Pulyani, Ya Karyata Wannan Zancen Da Ake Yadawa.
Sakon Da Ake Yadawa Shine Kamar haka.
SANARWA TA KARSHE”
Kada ku yi banza don Allah ku karanta
da kyau” Sannu, ni VARUN PULYANI
Daraktan WhatsApp ne, wannan post din
shine don sanar da duk masu amfani damu cewa mun sayar da WhatsApp ga
Mark Zuckerberg akan dala biliyan 19.
Yanzu Mark Zuckerberg ne ke sarrafa
WhatsApp.
Idan kuna da akalla lambobi
20, aika wannan sms kuma tambarin ku
na WhatsApp zai canza zuwa sabon
gunki tare da “f” na Facebook a cikin
awanni 24. Tura wannan sako ga
mutane sama da 10 don kunna sabonWhatsApp dinku tare da ayyukan
Facebook ko kuma asusunka za a goge
daga sabbin sabobin.
Wannan ita ce shawara ta karshe!Barka da warhaka, da alama duk
gargadin gaskiya ne, ta amfani da kudin
kudin WhatsApp daga lokacin bazara na
2017. Idan kun aika wannan tashar zuwa20 daban-daban akan jerinku, alamar ku
za ta zama shudi kuma za ta zamakyauta a gare ku. Idan ba ku yarda da ni
ba ku gani gobe da karfe 6 na yamma na
kare WhatsApp kuma dole ne ku biya don
bude shi, bisa doka ne wannan post din
don sanar da duk masu amfani da mu,
sabobin mu sun cika cunkoso a kwanan.
Ko Kuma Sakon Murya Na Hausa Dana Turanchi Wanda Na Hausa Yana Kaiwa Tsawon Minti Daya Da Sakan Arba’in Na Tiranchi Kuma Minti Biyu Da Sakan Arba’in
Wannan Sakon Ba Gaskiya Bane Kuma Ankaryatashi Duk Wanda Aka Turawa Ba Sai Ya Turawa Wani Ba Kawai Kuna Sharar Da Al’amarin.
Munaso ku Watsa Labarin Nan Domin Yaje Kunnen Mutane Da Basusan Halin Da Ake Ciki Ba Akan Wannan Al’amari, Sannan Kada Ku Manta Ku Danna Alamar Kararrawa Domin Samun Sababbin Shirye-shiryenmu Akoda Yaushe Mungode.
Ku Karanta Wannan Labarin:
Yanzu Yanzu Nan Kotu Ta Dakatar Da Sabon Sarki Katagoro A Jihar Neja Muhammad Na Bakwai
Ya Kashe Makudan Kudade Saboda Halittarsa Ta Zama Kamar Ta Dabba