Da mawaka da masu zaman banza marasa sana’a duk daya suke, cewar Alhaji Shu’ibu galadima

Da mawaka da masu zaman banza marasa sana'a duk daya suke, cewar Alhaji Shu'ibu galadima

Alhaji shu’ibu umar galadima wanda shugaban Yamaltu Deba ne yayi kira ga mawaka kan cewa su kama sana’a, domin ya bayyana cewa da mawaka da masu zaman banza duk daya suke.

Shugaban karamar hukumar ta Yamaltu Debe Alhaji shu’ibu galadima ya bayyana hakan ne a lokacin da kungiyar mawakan karamar hukumar ta Yamaltu Debe suka kai masa ziyarar ban girma zuwa ofishin sa dake Debe na karamar hukumar Yamaltu Debe dake jihar Yobe, kamar yadda Barewaradio suka ruwaito.

Shu’ibu galadima ya kara da cewa, waka ba sana’a bace sannan kuma ni a matsayina na dan siyasa waka bata isa tasa naci mulki ba ko kuma na fadi, sabida haka ina mai bawa mawaka shawara dasu tashi su kama sana’a a matsayin su na matasa.

Sai fai wannan bayani na Shu’ibu galadima bai yiwa mawakan kungiyar dadi ba inda, kamar yadda mataimakin shugaban kungiyar Nazeer Alhaji waka ya bayyana cewa, gaskiya wannan abin da aka mana bamuji dadi ba ko babu komai ai munkawo masa ziyara ya kamata ace yayi godiya da irin wannan girmamawar da muka masa, amma bai yi hakan ba sai ma yayi ta zagin sana’ar waka tare da kushe ta.

Nazeer Alhaji waka yace, kuma ko yana so ko baya so mawaka suna bada cikyakkiyar gudunmawa wajan cigaban al’ummar duniya musamman ma ga ‘yan siyasa.

Daga karsge Nazeer Alhaji waka yayi kira ga mawaka da suyi watsi da wannan maganar, sannan kuma susa gaskiya da tsaron Allah a cikin sana’ar su ta waka domin ya fadi cewa, ako wace sana’a akwai wuta sannan kuma akwai aljannah.

Karanta wannan labarin.

Kowane musulmin duniya dan izala ne kawai dai iskancin banza ne irin na mutane, cewar jarumi Sulaiman bosho

Karanta wannan labarin.

Allahu akbar: Ashe wadannan abubuwan sukayi silar rasuwar wasu daga cikin jaruman kannywood

Karanta wannan labarin.

Na daina saka sabbin jarumai mata a shirin fim dina kwanda suyi wata sana’ar ko suyi aure, cewar Abubakar bashir mai shadda

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button