Gwamnan Jihar anambara yasha da kyar a harin da Ake zargin ‘yan Biafra ta IPOB.

Gwamnan Jihar anambara yasha da kyar a harin da Ake zargin 'yan Biafra ta IPOB.

Yan bindiga sun kai hari ga jerin motocin gwamna Willie Obiano na Anambra tare da tsare su na tsawon awa daya.

To Gwamnan anambara yasha da kyar a wajan ‘yan Bindiga Wanda suka kaimar Hari Cikin jerin motocin gwamna.

A na zargin kungiyar yan awaren Biafra ta IPOB da kai harin, a lokacin da suka tarwatsa taron kamfe da jam’iyyar APGA ta shirya a makarantar sakandaren Otada da ke karamar hukumar Ihiala yau Talata.

Kamar yadda wani mazauni garin ya shaida wa Jaridar Daily Trust, ayarin gwamnan ya shafe awa daya hannun IPOB, kuma an rika jin harbe-harbe a lokacin da su ke tsare da tawagar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sanda a jihar Anambra DSP Tochukwu Ikenga ya tabbatar da cewa an kai hari a karamar hukumar Ihiala.

A sanarwar da jami’in ya fitar ya ce rundunarsu ta dakile harin da a ka kai a Otada, inda ta kwato makamai da motoci a hannun maharan.

A martanin da gwamnati ta mayar ta hannun kwamishinan yada labarai C.Don Adunuba, ta ce jami’an tsaro sun yi namijin kokari wurin dakile harin bayan musayar wuta da maharan.

To jama’a zamu so mukarbi ra’ayoyinku akan wannan harin dayafaru Wanda  jami’an tsaro sukayi musayar wuta.

KU KARANTA WANNAN:

Na daina saka sabbin jarumai mata a shirin fim dina kwanda suyi wata sana’ar ko suyi aure, cewar Abubakar bashir mai shadda

NDLEA tayi Nasarar Kama Mutane 134 a Jihar jigawa cikinsu harda.

Yadda Akayi Birthday Din Halima Buhari Babbar Yar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

Kashi 50% Cikin 100% Mata a Nigeria Basa amfani da internet Wanda wannan ya kawo.

Kada kumanta kudanna Mana alamar kararrawar sanarwa Domin samin Jin kararrawar shirye-shiryanmu masu kayatarwa mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button