An garkame wani matashi mai suna Sadi bala lamido dalilin wani rubutu daya wallafa a Facebook akan Gwamnan Kano

An garkame wani matashi mai suna Sadi bala lamido dalilin wani rubutu daya wallafa a Facebook akan Gwamnan Kano

Kotun majistret mai lamba goma 10 wanda take karkashin mai shar’a, Muhammad jibrin, ta tura wani mutumi gidan gyaran hali.

Mutumin mai suna, Sadi bala lamido, an kamashi ne da zargin sakin baki akan Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi umar ganduje.

Sadi bala lamido ya wallafa rubutun a kafar sada zumunta ta Facebook inda yayi wasu kalamai a cikin rubutun marasa kan gado, inda wasu suke zargin cewa da Gwamnan jihar Kano yake Dr Avdullahi umar ganduje, kamar yadda Freedom Radio ta fitar da wannan bayanin.

A lokacin da aka karantawa Sadi bala lamido wannan tuhumar da ake masa sai ya musanta wannan zargin, inda lauyansa wanda yake kare shi ya roki kotun data bada damar ayi belin shi.

A nan ne lauyan Gwamnati mai suna barista Lamido soron dinki ya bayyana cewa yana da suka sannan kuma kotu ta sanya wata ranar, domin ya zaiyi suka akan rokon bayar da belin da za’a yi.

Wakili Yusuf nadabo isma’l ya fadi cewa, kotun ta tsayar da ranar 15 ga wannan watan da muke ciki, domin lauyan Gwamnati Lamido soron dinki ya gabatar da sukan da zaiyi a kan rokon neman beli.

Karanta wannan labarin.

Tabbas Rike Waya A Hannun Budurwa Kuma ‘Yar Talakawa Yana Da Matukar Hatsari A Yanzu Cewar Masana Rayuwar Dan Adam

 Karanta wannan labarin.

Allah Yayi Mata Rasuwa Bayan Neman Yafiyar Mutane A Facebook ~ Aeshart Muhammad Nasara

Karanta wannan labarin.

An Karyata Sakon Da Ake Turawa Na Rufewa Whatsapp Din Mutane

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button