Squid Game: Yadda Aka Tattauna Kan Film Din Da Aka Kalleshi Sau Miliyan 111 Acikin Kwana 28 A Nigeria
Squid Game: Yadda Aka Tattauna Kan Film Din Da Aka Kalleshi Sau Miliyan 111 Acikin Kwana 28 A Nigeria

Ga Masu Shiga Shafin Netflix Domin Kallon Kayatattun Fina-finan Kasashen Waje Da Kuma Manyan Fina-finan Nigeria Masu Shahara, Zasu Ga Ana Yawan Kallon Wani Kayataccen Shirin Film Mai Dogon Zango Wato Squid Game.
Bayan Fitowar Wannan Shirin Film Sai Akayi Sa’a Ya Karbu A Wajen Mutane Duba Da Irin Chakwakiyar Datake Cikinsa, Tare Da Wasu Abubuwa Masu Daukar Hankalin Mai Kallo.
Film Din Mai Dogon Zango Wato Squid Game Ya Samu Karbuwa Da Yawa Daga Wajen Mutane Yadda Aka Samu Mutanen Dasuka Kalli Film Din Mutum Miliyan 111 Acikin Kwana 28.
Ganin Haka Yasa Mutane Da Dama Suke Ta Tattauna Batu Akan Film Din, Acikin Mutanen Dasuke Tattaunawa Har Da Wasu Daga Cikin ‘yan Nigeria.
Kamar Yadda Cikakken Rohoto Ya Sanar
A shafin Facebook a Najeriya bayanai sun nuna an yi maganar fim ɗin sau kusan da 150,000 a Yan kwanakin nan.
A shafin Instagram kuma bayanan sun nuna a fadin dunyiya an yi amfanid a maudu’in Squid Game Sau sau 732,183.
Duk an san da fitowar fim ɗin, amma a yanzu ya tabbata a hukumance: Squid Game ya zami shi ne gagrumin fim mai dogon zango da kamfanin Netflix ya taɓa ƙaddamarwa.
An kalli diramar ta ƙasar Koriya sau miliyan 111 a kwanaki 28 na farko inda ya doke shirin Bridgerton da a yake kan gaba da miliyan 82.
An lissafa yawan waɗanda suka kalli fim ɗin ne ga duk wanda ya kalli minti biyun farko.
Mataimakin shugaban Netflix na Koriya da Kudu maso gabashin Asiya da Australiya da New Zealand ya ce shirin ya samu gagarumar nasara “fiye da zatonmu.”
Minyoung Kim ya shaida wa CNN cewa: A lokacin da muka fara zuba jari kan shirye-shirye da fina-finan Koriya a 2015, mun san cewa so muke mu yi abin da zai jawo hankalin mutane a yankin Koriya da Asiya da ma duniya baki ɗaya.
“A yau, fim din Squid Game ya zama gagara gasa fiye da mafarkinmu.”
Shirin mai zango tara, wanda aka fara a watan Satumba, yana ba da labarin wata kungiyar wasu dan bana bakwai ne suke yin irin wasannin yara wato games.
Akwai kyauta ta dala biliyan 45.6 da aka sanya ga wanda ya ci, wadda ba za ka ji haushin rasa kyautar ba sai lokacin da ka fadi a wasan kuma aka kashe ka.
Kowa magana yake a kan fim din Squid Game kama daga kan fitattun mutane zuwa mashahuran dan kwallo.
Tarurarin cikin fim din sun yi suna a duniya – Jung Ho-yeon wanda ya fito a matsayin Sae-byeok ya samu mabiya miliyan 14 a Instagram.
Zamu So Mu Karbi Ra’ayoyinku A Sashenmu Na Tsokaci Akan Wannan Shirin Film Din Mai Dogon Zango Wato Squid Game.
Kada Ku Manta Ku Danna Alamar Kararrawa Domin Samun Sababbin Shirye-shiryenmu Akoda Yaushe Mungode.
Ku Karanta Wannan Labarin:
Wannan Babban Darasine Ga Wayanda Basu San Makiryicin Yan Damfara Da Artificial Karuwai Ba
Ku Karanta Wannan Labarin:
Yadda Baturiya ‘yar kasar Amurka ta bukaci matashi dan Nageriya yayi wuff da ita domin tana san shi
Ku Karanta Wannan Labarin: