Wani Mutumi Ya Kashe Abokinsa Bayan Ganinsa Yana Lalata Da Matarsa A Mafarki
Wani Mutumi Ya Kashe Abokinsa Bayan Ganinsa Yana Lalata Da Matarsa A Mafarki

Lamarin Ya Auku Ne A Kasar Ghana Bayan Da Mutumin Yayi Mafarki Abokinshi Yana Lalata Da Matarsa A Mafarki Yayi Masa Kisan Gilla.
Kamar Yadda Jarida Vanguard Ta Rawaito Ana Zargin Mutumin Da Kashe Abokinsa, Bayan Ya Ganshi A Mafarki Yana Saduwa Da Matarsa.
Rundunar Yan Sanda Kasar Ghana Ta Kama Wani Mutum Mai Suna Kwado Adusei Wanda Akafi Sani da Desco,Da Laifin Kashe Abokinshi A Wawase Cikin Garin Afigya Kabre, Dake Yankin Kudanchin Ashanti A Cikin Kasar Ta Ghana.
Wanda Ake Zargin Yayiwa Abokinshi Kisan Gilla Bayan Ganinsa A Mafarki Yana Lalata Da Matashi.
Desco Ya Kashe Abokinnashi Mai Suna kwesi Banahene, Bayan Ya Jashi Cikin Daji Sannan Yayi Ta Caka Masa Wuka Ajikinshi Har Ya kasheshi.
Daga Baya Aka Tsinci Gawar Banahene Acikin Daji, Inda Desco Ya Kasheshi Lokacin Da Aka Tsawaita Bincike Bayan Daukan Tsawon Lokaci Ba’a Ganshi Ba.
Haka Kuma Wanda Ya Kashe Abokinnasa Wato Desco Ya Taba Yunkurin Kashe Kakansa, Biyo Bayan Zarginsa Da Yake Na Sace Masa Mazakuta Shiyasa Baya Jimawa A Gado.
Sai Dai Kuma Kakannashi Ya Rayu Bayan Samun Kulawa Ta Musamman Daga Likitoci.
Acikin Bayanin Desco Ya Bayyana Cewa A Duk Lokacin Da Yayi Mafarki Yana Zama Gaskiya, Shiyasa Yayi Sauri Ya Dauki Mataki Akan Mutanen Da Yake Ganin Zasu Ayyana Wani Abu Da Zai Bata Masa Rai, musamman Wannan Abokinnasa Daya Ganshi Yana Saduwa Da Matarsa, Bayaso Yaga Abun A Zahiri Shiyasa Yayi Sauri Ya Dauki Mataki Akan Haka.
Toh Allah Ya Kyauta Zamu So Mu Karbi Ra’ayoyinku A Sashenmu Na Tsokaci Akan Wannan Al’amari Sannan Kada Ku Manta Ku Danna Alamar Kararrawa Domin Samun Sababbin Shirye-shiryenmu Akoda Yaushe Mungode.
Ku Karanta Wannan Labarin:
Bayyanar Bidiyon Mataimakin Gwamnan Sokoto Acikin Hotel Da Matarsa Ya Dauki Hankula
Ku Karanta Wannan Labarin:
Tirkashi Jaruma Maryam Booth Ta Kama Saurayin Dayake Bata Mata Suna A Duniya Yanzu
Ku Karanta Wannan Labarin: