An dakatar da Babban taron APC a Jihar Oyo bisa zargin wasu ‘yan jamiyya dayin magudi
An dakatar da Babban taron APC a Jihar Oyo bisa zargin wasu 'yan jamiyya dayin magudi

Tofa gudanar da Cikin rashin gaskiya shine Babban dalilin da yasa aka dakatar da zaban.
Wannan na Daya daga Cikin Dalilan dayasa aka dakatar dazaban a wannan lokacin biyo bayan rashin gaskiya datake Shirin aukuwa.
Shugabancin jam’iyyar APC na ƙasa mai mulki a Najeriya ya dakatar da babban taron jam’iyyar a Jihar Oyo saboda zargin yunƙurin maguɗin zaɓe.
Shugaban APC na riƙo, Gwamna Mai Mala Buni, shi ne ya sanar da matakin cikin wata sanarwa da sakataren jam’iyyar, John James Akpanudoedehe, ya fitar a safiyar Asabar.
Ya ce dakatarwar ta zama dole domin aiwatar da zaɓen shugabannin jam’iyyar cikin gaskiya a Oyo. Ana zargin wasu ‘ya’yan jam’iyyar da buga takardun zaɓe na bogi, in ji sanarwar.
“Shugaban jam’iyya na ƙasa ya umarci kwamatin shirya taron a Oyo da su koma sakatariyar jam’iyyar domin tattaunawa,” a cewar sanarwar.
Jam’iyyar APC na gudanar da taruka a faɗin Najeriya da zummar zaɓen shugabanninta a kowane mataki yau Asabar.
To jama’a zamu so mukarbi ra’ayoyinku akan wannan lamarin na siyasar gida Domin Jin tabakinku akan wannan lamarin zaku iya biyomu a sahinmu na tsokaci.
KU KARANTA WANNAN:
Soyayya tsakanin mawaki Hamisu breaker da jaruma Sadiya adam ta dauki hankulan jama’a
Jerin shahararrun jaruman kannywood wanda suka taba fitowa takarar siyasar Nageriya
To jama’a kada kumanta kudanna Mana alamar kararrawar sanarwa Domin samin Jin kararrawar shirye-shiryanmu masu kayatarwa mungode.