Fatalwa Ayshert Muhammad Nasara tayiwa Datti Assalafy zazzafan martani akan kazafin daya mata

Fatalwa Ayshert Muhammad Nasara tayiwa Datti Assalafy zazzafan martani akan kazafin daya mata

Bayan labarin mutuwar Ayshert muhammad nasara ya dauki hankulan jama’a a kafar sada zumunta Facebook, inda daga baya akace karya ne ‘yar damfara ce bata mutu ba.

Inda hakan ya dauki hankulan jama’a da dama har ma kowa ya fara fadin albarkacin bakin sa, amma daga karshe fatalwar tayi magana inda take bawa mutane hakuri kamar haka.

Salamu alaikum, game da labarin mutuwata ba haka bane, Maryam usnan ce ta fara yadawa, kuma wallahi bani na umarceta ta aikata hakan ba, wannan sabani muka samu shine ayi amfani da wannan hanyar domin ramuwa.

Wallahi summa tallahi ba wanda na damfara, duk wanda yamin wannan kazafin kuma Allah ya isah.

Dan Allah kuyi hakuri bisa hankalin da aka tada muku, albarkacin Annabi Muhammad S.A.W, nagode.

To amma sai dai ba ana gizo ke sakar ba, sai gashi kuma tana yiwa Datti assalafy raddi da martani akan cewa yayi mata kazafi inda ta wallafa kamar haka.

Wallahi muhammad nasara shine sunan mahaifina.

Kuma sai yau na tabbatar da Datti assalafy bakasan aikinka ba.

Idan akwai wanda na damfara, inso ka bayyanawa duniya sunansa, hoton sa, meye na damfareshi, idan bakayi haka ba Allah ya isa tsakanina da kai.

Sannan kuma ta sake bayyanawa duniya cewa, duk wanda yace ta damfare shi to yayi magana inda tayi rubutun kamar haka.

Duk wanda yace ba damfareshi dan girman Allah yafito ya nuna kansa.

Muhammad nasara sunan mahaifina ne, wanda asalinsa Jalingo ne, But yafi shekara goma yana Abuja.

Ina da hadi da gumel tabbas, duk mai son amsa yabiyoni private, na masa alkawarin fadar gsky.

Karanta wannan labarin.

Abin kunya ne ace ‘yan kannywood sun kasa daukar nauyin Hamza yahaya akan rashin lafiyar sa, Duniyar kannywood

Karanta wannan labarin.

Yanzu – Yanzu Akayi Babbar Mutuwar Data Firgita Hankalin Mutane Da Dama innalillahi Matar Abubakar Gumi Ta Rasu

Karanta wannan labarin.

Allah sarki: Za’a sakewa jarumi Hamza yahaya aiki a hancin sa yana neman taimakon al’umma

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button