Jerin shahararrun jaruman kannywood wanda suka taba fitowa takarar siyasar Nageriya

Jerin shahararrun jaruman kannywood wanda suka taba fitowa takarar siyasar Nageriya

Kamar yadda kuka sani masana ‘antar shirya fina-finai ta kannywood ta tara jarumai maza da mata da dama a cikin ta, wanda har wasu daga cikin jaruman suka nemi takarar siyasa.

A yanzu ne zaku san jarumai guda biyar 5 wanda suka taba neman takarar siyasar Nageriya, wadannan jaruman sun fito takara a matakai daban-daban na yankunan da suke ciki, sannan kuma a dikar kasa kowa yana da damar da zai iya fitowa takara idan har ya cike ka’idojin hukumar zabe mai zaman kanta wato INEC.

Ga sunayen jaruman da suka nemi takarar siyasar domin su sami wani matsayi a yankunan su.

(1). Hamisu iyantama:

Hamisu iyantama ficaccan jarumi ne a msana’antar shirya fina-finan hausa ta kannywood wanda an jima ana damawa da shi, sannan kuma jarumin ya taba fitowa a takarar Gwamnan jihar Kano a shekarar 2007.

Hamisu iyantama ya fito wannan takarar ne a karkashin jam’iyyar ND, amma sai malam ibrashim shekarau ya kashe wannan zaben da za’ayi a lokacin.

(2). Alhassan kwalle:

Alhassan kwalle shima jarumi ne a masana’antar kannywood wanda yake fitowa a shirin barkwanci sannan kuma yana daya daga cikin masu ruwa da tsaki a masana’antar kannywood.

Alhassan kwalle ya nemi takarar siyasa da dama wanda a ciki har da takarar shugaban karamar hukumar Ungogo wanda ya nema a shekarar 2007 a karkashin jam’iyyar PDP, amma a wannan lokacin ya kare a mastayin dan takarar mataimaki.

Sannan kuma ya tsaya a takarar kansila a gundumar sa bachirawa da Ungogo karkashin jam’iyyar APC a shekarar 2015.

(3). Nura hussain:

Nura hussain shima yana daya daga cikin jaruman kannywood wanda ya jima yana kata rawar gani a cikin masana’antar, inda ya fito takarar kansila a mazabar Yakasai a karamar hukumar birni da kewayen ta cikin jihar Kano a shekarar 2007.

(4). Abba El-mustapha:

Abba El-mustapha jarumi ne a kannywood wanda yayi tashe sosai kuma ya jima a masana’antar kannywood.

Inda ya nemi takarar dan majalistar jiha mai wakiltar mazabar Gwale dake jihar Kano karkashin jam’iyyar PDP a shekarar 2015.

Amma Abba El-mustapha bai sami nasara ba domin kuwa bai mallaki tikitin tsaywa takatar ba tun a wajan zaben fidda gwani.

(5). Lawan ahmad:

Jarumi lawan ahmad wanda ya jima yana fitowa a shirin fina-finan masana’antar kannywood sannan kuma har kawo yanzu tauraruwar sa tana haskakawa, a yanzu haka lawan ahmad shine furodusan fim din nan mai dogon zango wato Izzar so.

jarumi Lawan ahmad ya taba neman tikitin takarar siyasa ta dan majalistar jihar Katsina mai wakiltar mazabar Bakori karkashin jam’iyyar APC amma bai yi nasarar samin tikitin ba.

Karanta wannan labarin.

Karanta wannan labarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button