Mutane goma Sha biyune 12 suka rasa ransu saka makon harin ‘yanbindiga a Jihar zamfara.

Mutane goma Sha biyune 12 suka rasa ransu saka makon harin 'yanbindiga a Jihar zamfara.

A kalla mutane 12 ne suka mutu a kyauyen Sakajiki na Masarautar Kauran Namoda ta Jihar Zamfara, biyo bayan wasu hare-haren yan Bindiga.

Kakakin rundunar yan sandan Jihar Muhammad Shehu, shine ya tabbatar da hakan ga gidan Talabijin na Channels Tv a jiya.

A cewarsa, adadin mutanen da aka kashe zai fi hakan, inda ba’a tura karin Jami’an tsaro wurin ba akan Lokaci.

Kakakin Rundunar ya ce Kwamishinan Yan Sanda na Jihar Zamfara ya sake tura karin Jami’an tsaro a yankin domin sake karfafa doka.

Wani shaidar gani da Ido, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 9 na Daren ranar Alhamis a lokacin da yan bindigar suka kwashe fiye da a wanni suka harbe-harbe a yankin.

A cewarsa, kimanin mutane 12 ne suka mutu a lokacin, kuma yan bindigar sun cigaba da aika-aikar har zuwa karfe 4 na safiyar ranar Juma’a.

Haka kuma ya ce yan bindigar sun kone shaguna da gidaje, da kuma Ofishin yan Sanda, da kuma sauran ababen hawa.

To jama’a zamu so mukarbi ra’ayoyinku akan aukuwar wannan lamarin Domin jintabakinku zaku iya biyomu kaitsaye ta shafinmu na tsokaci.

KU KARANTA WANNAN:

Fatalwa Ayshert Muhammad Nasara tayiwa Datti Assalafy zazzafan martani akan kazafin daya mata

 

Wa dannan sune dalilin dayasa ilimi yazama koma baya a Nigeria Wanda har suka janyomana

Abin kunya ne ace ‘yan kannywood sun kasa daukar nauyin Hamza yahaya akan rashin lafiyar sa, Duniyar kannywood

 

Yanzu – Yanzu Akayi Babbar Mutuwar Data Firgita Hankalin Mutane Da Dama innalillahi Matar Abubakar Gumi Ta Rasu

 

Allah sarki: Za’a sakewa jarumi Hamza yahaya aiki a hancin sa yana neman taimakon al’umma

Kada kumanta kudanna Mana alamar kararrawar sanarwa Domin samin Jin kararrawar shirye-shiryanmu masu kayatarwa mungode.

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button