Wa dannan sune dalilin dayasa ilimi yazama koma baya a Nigeria Wanda har suka janyomana

Wa dannan sune dalilin dayasa ilimi yazama koma baya a Nigeria Wanda har suka janyomana

Manyan Dalilan dayasa ilimi yazama koma baya a Nigeria Wanda Hakan yataimaka wajan Janyo duk abin da take faruwa a kasar.

Rahotan nabiyowa bayan wannan batune bayan wata fira da Daya daga Cikin manema labara.

Kwamishinan Ma’aikatar Ilimi, Kimiyya Da Fasaha ta Jihar Jigawa Dr Lawan Yunusa Danzomo, ya ce rashin samun Isassun kudade na daya daga cikin abubuwan da suka lalata fannin Ilimi a Kasar nan.

Dr Lawan Yunusa Danzomo, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a Cibiyar Horas da Ma’aikata ta Manpower dake Duste.

 

A cewarsa, bayan zuwan Gwamna Badaru Abubukar, gwamnati Jiha tayi nasarar gano wasu daga cikin matsalolin Ilimin Jihar nan, wanda suka hada da rashin kudade a fannin da rashin gine-gine masu kyau, da kuma karancin Ajujuwa da Malamai.

Haka kuma ya ce gwamnatin Jiha ta kashe Naira Biliyan 20 wajen inganta Ilimin Makarantun Firamare da Sikandiren Jihar nan cikin shekaru 6 da suka gabata.

Kwamishinan ya kara da cewa sunyi nasarar gina Makarantun Firamare 337, da kuma sabbin Kananan Makarantun Sikandire 130 wanda aka kirkira.

Kazalika, ya ce gwamnatin Jiha ta gina sabbin Ajujuwa dubu 6,679 da samar da Kujeru dubu 185,086 da kuma Kujerun Malaman Makaranta dubu 5,963 da aka samar a jihar nan.

Kwamishinan ya ce an gina gidaje 254 ga Malaman Makaranta da kuma Bandakuna dubu 1,418.

Kada kumanta Kuna tare Dani A.Usman Ahmad a shafinmu na Dalatopnews kucigaba da bibiyarmu Domin samin labaran Duniya kaitsaye.

KU KARANTA WANNAN:

 

An dakatar da Babban taron APC a Jihar Oyo bisa zargin wasu ‘yan jamiyya dayin magudi

 

Wani bawan Allah zai kai Hamza yahaya kasar waje domin a sake masa aiki a fuskar sa dalilin baya iya shan nunfashi sosai

Masoyin Hadiza Gabon Yayi Kaca Kaca Da Datti Assalfy Kan Munanan Kalaman Da Ya Jafeta Dasu

Kada kumanta kudanna Mana alamar kararrawar sanarwa Domin samin Jin kararrawar shirye-shiryanmu masu kayatarwa mungode.

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button