Yanzu – Yanzu Akayi Babbar Mutuwar Data Firgita Hankalin Mutane Da Dama innalillahi Matar Abubakar Gumi Ta Rasu
Allah Yayiwa Matar Marigayi Sheik Abubakar Gumi Rasuwa Wato Hajiya Aminatu Bintu

Marigayiyar Ta Amsa Kiran Mahallicinta A Yau Asabat 16,Ga Watan Oktoba A Shekara Ta 2021, A Wata Wallafa Da Sheik Ahmad Gumi Ya Fitar A Shafinsa Na Facebook.
Matar Wanda Mahaifiyace Ga Birgediya Janar Abdulkadir Gumi, Kuma Za’a Yi Jana’izzar Karfe 4:30 Na Yammah A Yau.
Dr Ahmad Gumi Ya Wallafa Wata Sanarwa Kamar Haka A Shafinsa Na Facebook Yadda Yake Bayyanawa Al’ummah Mutuwar Matar Ga Abunda Ya Wallafa.
Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun.
Allah yayiwa Hajiya Aminatu Bintu rasuwa. Matar Marigayi Sheikh Abubakar Gummi, dazu da safe. Mahaifiyar su Brigadier General Abdulkadir Gumi.
Za ayi Janazarta anjima a gidan Sheikh Abubakar Gumi da karfe 4.30 pm bayan Sallar La’asar.
Allah ya jikanta ya gafarta mata da sauran al’umma baki daya amin.
Salisu Hassan Webmaster
08038892030
16/10/2021
To Allah Ya Jikanta Ya Kuma Gafarta Mata Idan Tamu Tazo Allah Yasa Mu Cika Da imani Ameen.
Sannan Munaso Ku Watsa Labarin Nan Domin Yaje Kunnen Mutane Da Dama Domin Suji Wannan Babban Rashi Da’akayi.
Kada Ku Manta Idan Wannan Shine Karonka Na Farko A Wannan Shafin Munaso Ku Danna Alamar Kararrawa Domin Samun Sababbin Shirye-shiryenmu Akoda Yaushe.
Ku Karanta Wannan Labarin:
Allah sarki: Za’a sakewa jarumi Hamza yahaya aiki a hancin sa yana neman taimakon al’umma
Ku Karanta Wannan Labarin:
An dakatar da Babban taron APC a Jihar Oyo bisa zargin wasu ‘yan jamiyya dayin magudi
Ku Karanta Wannan Labarin:
Masoyin Hadiza Gabon Yayi Kaca Kaca Da Datti Assalfy Kan Munanan Kalaman Da Ya Jafeta Dasu