Tirkashi Shugaban ‘yansandan Nigeria yaba da Umarnin a Kamo ‘yansandan dasuke karbar cin hanci a kan titi biyo bayan video da yafita jiya a sabat.

Tirkashi Shugaban 'yansandan Nigeria yaba da Umarnin Kano 'yansanda dasuke karbar cin hanci a kan titi biyo bayan video da yafita jiya a sabat.

Cin hanci bakomai bane a wajan ‘yansada da sojojin Nigeria ba.

A yau da misalin karfe 12:00pm Shugaban yansanda Nigeria yabada Umarnin akamo wasu ‘yansanda da aka Kama da laifin karbar cinhanci.

Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya IGP Usman Alkali Baba ya bayar da uamrnin ƙaddamar da bincike kan ‘yan sandan da aka gani a bidiyo waɗanda aka zarga da yi wa wani matashi ƙwace.

Cikin bidiyon da ya karaɗe shafukan sada zumunta a jiya Asabar, ana iya jin wanda ke ɗaukarsa na cewa ‘yan sandan sun tsare matafiya ne inda suka zaƙulo wani matashi ɗauke da kwamfuta suka cusa shi a motarsu.

Kazalika ya yi zargin cewa ‘yan sandan sun nemi ya ba su kuɗi amma ya ce ba shi da su a matsayinsa na ɗalibi.

Duk da haka suka ce ya buga waya a turo masa ta banki domin su cire a na’urar ATM.

Mai maganar ya ce lamarin ya faru ne a garin Okene na Jihar Kogi da ke tsakiyar Najeriya.

Cikin wata sanarwa da kakakin ‘yan sanda na ƙasa Frank Mba ya fitar, “IGP Usman Baba ya umarci rundunar reshen Jihar Kogi da ta ƙaddamar bincike nan take”.

“IGP ya buƙaci a kwantar da hankali, yana mai cewa za a tabbatar da adalci da zarar an kammala binciken sannan a gurfanar da ‘yan sandan da aka kama da laifi a gaban kotu,” in ji sanarwar.

A lokuta da dama, ana zargin ‘yan sandan Najeriya da cin zarafin ‘yan ƙasa, abin da ya jawo gagarumar zanga-zangar EndSars a kasar kenan a 2020 wadda ta yi sanadiyyar rushe rundunar SARS ta ‘yan sandan. 

To mudai saidai muce Allah yakiyaye gaba to jama’a zamuso muji ra’ayoyinku akan aukuwar wannan lamarin a man gida Nigeria sabida irin wannan Yana faruwa a yankuna da Dama a dadin kasarnan Wanda yakamata Gwamnatin ta dau mataki akan wannan lamarin Dan kawa cigaba a kasarnan.

KU KARANTA WANNAN:

Wani mutumi ya yiwa Datti Assalafy zazzafan martani kan wasu maganganu daya fada ga Hadiza gabon wanda basu dace ba

Saurari sabuwar wakar Naziru M Ahmad mai taken, Ja kulle da makulli, wanda ya wallafa ta a yanzu

Hadiza Gabon Ba Karuwa Bace, Ku Daina Tonawa Mutane Asiri Martanin Wani Mutumi Akan Datty Assalafy

Kada kumanta Kuna tare Dani A.Usman Ahmad a shafinmu na Dalatopnews sannan kada kumanta kudanna Mana alamar kararrawar sanarwa Domin samin Jin kararrawar shirye-shiryanmu masu kayatarwa mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button