Wani mutumi ya yiwa Datti Assalafy zazzafan martani kan wasu maganganu daya fada ga Hadiza gabon wanda basu dace ba
Wani mutumi ya yiwa Datti Assalafy zazzafan martani kan wasu maganganu daya fada ga Hadiza gabon wanda basu dace ba

Kowanne mai bibiyar shafukan sada zumunta da kuma kafafan yada labarai yasan labarin rigumar jaruma Hadiza gabon da Auwal isah west, dalilin wasu maganganu da yayi kan jarumar inda har takai ga tasa an kama shi.
Bayan kwana biyu da cece-kuce akan kama shin da jaruma Hadiza gabon tasa aka yi, sai Auwal isah west ya bayyana a cikin wata bidiyo inda yake bawa jarumar hakuri akan munanan maganganun daya jefeta da su.
Ya wallafa wannan bidiyon ne a shafin sa na sada zumunta instgram inda yake karyata kansa game da maganganun daya fada a kan jaruma Hadiza gabon, na cewa yasan kawalin ta da dai sauran abubuwan daya fada.
Daga baya kuma sai shahararran marubucin nan Datti Assalafy ya wallafa wani rubutu inda yake kalaman batanci akan jaruma Hadiza gabon, kusan irin kalaman da Auwal isah west ya fada akan jarumar.
Domin maganganun da Auwal isah west yayi a cikin wannan bidiyon jama’a da dama zasuyi zaton da gaske yake domin suna ganin shima dan cikin masana’antar kannywood din ne.
Sai kuma Datti Assalafy yayi munanan kalamai akan jaruma Hadiza gabon wanda har ma wasu mutanen suka ganin hakan bai dace ba, sannan kuma sukayi ta korafe-korafe akan abin daya fada.
Bayan wadannan kalamai da Datti Assalafy yayi akan jaruma Hafiza gabon sai aka sami wani mutumi, inda yayi tsokaci akan kalaman nasa tare da jan kunnen sa akan wadannan kalamai da yake fada ga jaruma Hadiza gabon.
A cikin wata bidiyo da muka samu a wata tasha dake kan manhajar Youtube mai suna, Brothers Intertaiment, zakuji muryar mutumin yadda yake fadan gaskiya akan maganar da ake yayatawa ga jaruma Hadiza gabon.
Ga bidiyon nan domin ku kalla kuji yadda mutumin yake bayani dalla-dalla.
Karanta wannan labarin.
Saurari sabuwar wakar Naziru M Ahmad mai taken, Ja kulle da makulli, wanda ya wallafa ta a yanzu
Karanta wannan labarin.
Hadiza Gabon Ba Karuwa Bace, Ku Daina Tonawa Mutane Asiri Martanin Wani Mutumi Akan Datty Assalafy
Karanta wannan labarin.
Jarumi Abba El-mustapha yayi cikekken bayani game da masu yada labarin cewa mahaifiyar sa ta rasu