Yanzu Yanzu: Rigima ta barke tsakanin jaruma Rahama kumo da daraktotin da suke sata a shirin Jamila makira

Yanzu Yanzu: Rigima ta barke tsakanin jaruma Rahama kumo da daraktotin da suke sata a shirin Jamila makira

Wani abu da yake nema zama ruwan dare shine yadda masu shirya shiri mai dogon zango suka yawan samin sabani da jarumai musamman jarumai mata masu jagorantar shirin, wanda irin haka ya sha faruwa a fina-finai da dama wanda suka shahara kamr su, Bugun zuciyar masoya, wanda a dalilin cire jaruma Hannatu usman dalilin da zagi darakta inda Lawan ahmad ya tsinketa da mari a wajan daukar shirin.

Sannan kuma a kwan-kwanan nan kunji yadda ta dalilin cire Ummi Rahab daga shiri mai dogon zango Farin wata sha kallo, aka dinga ‘yar tsama tsakanin ta da Adam a zango.

A yanzu ma irin hakace ta faru tsakamin jaruma Rahama kumo wacce aka fi sani da Jamila makira da darakta furodusan shirin Jamila makira, inda labarin ya fara yawo kan cewa an cire jaruma daga cikin shirin har ma tayiwa mashiryan shirin zagin tsamar nama, Rahama kumo dai indan bazaku manta ba itace jarumar da a kwanakin baya kuka sami labarin ta musulinta sanadiyar fim wanda tasha gwagwarmaya kamin ta sami damar fitowa a shirin jamila makira na kamfanin Brothers point muntimedia wanda yake zuwa a manhajar Youtube mai suna Makira Tv.

Domin jin yadda lamarin ya faru mun tuntubi jaruma Rahama kan wannan batu inda ita ma ta bayyana mana yadda ake jita-jita haka ita ma taji cewa an cireta a shirin bata da masiya kwai haka taga an fita location ba tare da an sanar da ita ba, sannan kuma alakarta ta dan yi sanyi tsakaninta da masu shirin domin takan yi musu magana basa amsawa don haka da taji jita-jita cewa an cireta sai ta yarda cewa abincin ta ya kare a a shirin.

Domin kuji cikekken yadda labarin yake sai ku kalli bidiyon da muka aje muku a kasa wanda tsahr Tsakar gida dake kan Youtube ta wallafa wannan labarin.

Ga bidiyon nan sai ku kalla kai tsaye.

Karanta wanna labarin.

Wani mutumi ya yiwa Datti Assalafy zazzafan martani kan wasu maganganu daya fada ga Hadiza gabon wanda basu dace ba

Karanta wannan labarin.

Saurari sabuwar wakar Naziru M Ahmad mai taken, Ja kulle da makulli, wanda ya wallafa ta a yanzu

Karanta wannan labarin.

Jarumi Abba El-mustapha yayi cikekken bayani game da masu yada labarin cewa mahaifiyar sa ta rasu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button