Trending

Cikakken tarihin Rahama Sadau da Asalin Addininta

Cikyakkyan tarishin Rahama Sadau da Asalin Addininta

Cikyakkyan tarishin Rahama sadau.

Tauraruwar Fim a Nijeriya (Nigerian Fim star), Mawakiya (singer) kuma ‘yar Rawa (Dancer), Mai daukar nauyin fina finai (producer), daya daga cikin shahararrun jarumai na Africa, Rahma Sadau. Ta fito a fina finai da suka yi fice a Kannywood da Nollywood baki daya.

An haifi Rahma Sadau ranar 7 ga watan Disamba 1993 (7th December, 1993) a garin Kaduna dake Arewa maso yammacin Nijeriya. Sadau ta shiga masana’antar Kannywood a shekarar 2013. Jarumar ta yi fina finai da yawa kafin ta shahara.

Fim din “Jinin Jiki Na” da Fim din “Gani Ga Wane” tare da Jarumi Ali Nuhu wato Sarki a Kannywood. Rahma Sadau ta sami Kyaututtuka da dama sakamakon rawar da ta taka a cikin fina finai daban daban. Jarumar tazo da salo iri daban daban da sauran jarumai basu da irin sa.
KARATUN JARUMA RAHMA SADAU:

Rahma Sadau tayi karatun Firamare da sakandire duk a Garin Kaduna daga nan ne Sadau ta wuce Makarantar gaba da sakandire dake Cyprus inda ta yi karatu fannin Bunkasa Rayuwar Dan Adam (Human Resources Management), a Makarantar ilimin Kasuwanci da tanadin Kudi (School of Business And Finance) dake Yammacin Mediterranean.

Rahma Sadau tayi shuhura sosai domin tana daya daga cikin manyan jarumai da aka dogara dasu a Masana’antar Kannywood

KALUBALEN DA JARUMAR TA FUSKANTA:

A shekarar 2016, hukumar ladabtar da masu karya dokoki ta kasa reshen Kannywood wato (Motion Pictures Practitioners Association Of Nigeria (MOPPAN)) ta dakatar da Jarumar daga fitowa a fina finan Kannywood baki daya sakamakon wata waka da ta fito a ciki tare da mawakin gambara (hip hop) wato Klassic suna soyayyar da bata dace da al’adu da addinin Musulinci ba (romantic).

Shekara daya daga faruwar haka Jaruma Rahma Sadau ta rubuta takardar neman afuwa zuwa ga Hukumar MOPPAN.

A 2018 aka dage dakatarwar da aka yi mata sakamakon shiga tsakani da gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje yayi.

NASARORIN RAHMA SADAU:

Jaruma Rahma Ibrahim Sadau ta sami nasarori da yawa a rayuwarta musamman ma tun daga shigarta masana’antar Kannywood wanda ya jayowa iyaye da ‘yan’wanta zama abin alfahari. A 2016 ta kasance Jarumar da tafi kowace Jaruma yin fice a Kannywood (Face of Kannywood). A dai wannan shekarar Rahma Ibrahim Sadau ta fito a wani fim din turanci mai dogon zango a EbonyLife TV.

A 2017 Jaruma Rahma Ibrahim Sadau ta bude kamfani na kashin kanta mai suna Sadau Pictures inda ta shirya fim na farko mai suna Rariya, wanda ya kunshi Sharhararrun Jarumai kamar su Ali Nuhu, Sani Musa Danja, Sadiq Sani Sadiq, Aminu Sharif Momoh, Fati Washa da dai sauran su. Ta kuma fito a matsayin malamar makaranta a wani fim mai dogon zango na tashar MTV Shuga. A 2019 tashar taci gaba da shirin kashi na shida a Nijeriya inda Jaruma Rahma Sadau ta sake fitowa tare da wasu Jarumai kamar Su Yakubu Muhammad, Timini Egbuson, Uzoamaka Aniunoh da Ruby Akabueze.

Rahma Ibrahim Sadau tana kanne mata su uku wato Zainab Sadau, Fatima Sadau, Aisha Sadau, da kanen Haruna Sadau. Sadau ta shiga masana’antar Kannywood a 2003 ta hannu Jarumi Ali Nuhu kamar yadda muka fada muku tun da farko.
KYAUTUKAN SADAU:

Jarumar Jarumai mata (Kannywood) 2014.

Jarumar Jarumai mata (Kannywood) 2015.

Jarumar Jarumai mata (African Best Actress Award) 2017. Da sauran su.

FINA FINAN JARUMA SADAU:

Rahma Ibrahim Sadau ta fito a fina finai da yawa kamar:

Mai Farin Jini, Da Kai Zan Gana, Gani Ga Wane, Farin Dare, Suma Mata Ne, So Aljannar Duniya, Sirrin Dake Rai Na, Mati Da Lado, Sabuwar Sangaya, Alkalin Kauye, Ana Wata Ga Wata, Gidan Farko, Halacci, Hujja, Garbati, Kaddara Ko Fansa, Jinin Jiki Na, Wutar Gãba, Wata Tafiya, Sallamar So, Kasata, The Other Side, Sons of The Caliphate, TATU, Rumana, Rariya, MTV Shuga Naija, Ba Tabbas, Adam, Aljannar Duniya, Up North, Zero Hour, Kaddara Ko Fans, Kisan Gilla.

WAKOKIN JARUMAR SADAU:

Rahma Ibrahim Sadau ta yi wakoki da dama amma ga kadan daga cikin su:

  1. Zubar Hawaye
  2. Tuna Baya
  3. Dan Sarkin Agadez
  4. Sabo Da Mazan Kwarai
  5. Auren Jeka Nayi Ka
  6. Da sauran su.

Rahma Sadau ta kuma kafa gidauniyar tallafawa ‘yan’uwa mata masu karamin karfi.

Kada kumanta Kuna tare Dani A.Usman Ahmad a shafinmu na Dalatopnews kucigaba da bibiyarmu Domin samin labaran kannywood dakuma na Duniya bakidaya.

KU KARANTA WANNAN:

 

Yanzu Yanzu: Wata mata ta tona asirin jarumi Adam a zango da mawaki Ado gwanja akan kisan wasu yara 4

 

Sakamakon katsewar laying wayar MTN kamfani yabada Diya ga duk masu amfani da layinwaya Na MTN na Katin waya da Data.

 

Yanzu Yanzu: Rigima ta barke tsakanin jaruma Rahama kumo da daraktotin da suke sata a shirin Jamila makira

 

Tirkashi wannan shine Babban dalilin dayasa muke satar jariri nida Matata saboda.

Kada kumanta kudanna Mana alamar kararrawar sanarwa Domin samin Jin kararrawar shirye-shiryanmu masu kayatarwa mungode.

 

 

 

 

 

 

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button