Trending

Kalli Halin Da Sarkin Bagudu Ya Kasance Bayan Kubutarsa Daga Hannun ‘Yan Ta’adda Masu Garkuwa Da Mutane

Kalli Halin Da Sarkin Bagudu Ya Kasance Bayan Kubutarsa Daga Hannun 'Yan Ta'adda Masu Garkuwa Da Mutane

Kamar Yadda Kuka Sani A Kwanakin Baya Labari Ya Karade Kafafen Sada Zumunta Na Bacewar Sarkin Bagudu, Biyo Bayan Da Masu Garkuwa Da Mutane Suka Saceshi.

A Wani Dogon Bayani Da Muka Samu Daga Shafin Instagram Na Garkuwar Arewa Sun Wallafa Hoton Sarkin Bagudu Cikin Matsananchin Hali Bayan Kubutarsa Daga Hannun Yan Ta’adda.


Ga hoton Sarkin Bungudu (Sarkin Yanka Mai Daraja Ta
Daya) nan ya na ta yawo a kafafen sadar da zumunta,
bayan da Allah ya kubutar da shi daga hannun masu
garkuwa da mutane, wanda ya shafe tsawon kwanaki
talatin da biyu (32) a hannunsu.

(1) Abu ne mai matukar tayar da hankali, a ce
wadannan mutane har suna da karfin halin iya kama
Sarki Mai daraja ta daya, har suna da karfin ikon iya
rike Sarki mai daraja ta daya tsawon lokaci, an kuma
kasa bibiyarsu a amso shi.

(2) Wasu kafafun watsa labarai sun bayyana cewa ba
a sako Sarkin Bungudu ba sai da aka biya kudin fansa
kimanin naira miliyan ashirin (N20,000,000) lakadan
ba ajalan ba. (Vision FM, Farin Wata TV).

(3) Don Allah ku duba yanayin da Mai Martaba Sarki
ya samu kansa a ciki, ku yi la’akari da yadda ya fita
daga hayyacinsa.

Duba hotunan nan nasa da ya ke
cikin kayan alfarma na sarauta da kasaita, sannan ka
duba hoton da aka dauka bayan samun kubutarsa.

A gaskiya dukkan wani naui na tashin hankali da
barazana ya gama tabbata a Najeriya tuni.Lamarin wannan kasa ba abin wasa ba ne, lamuransun wuce dukkan yadda mutum ya ke sawwarawa
Wallahi.

Lamarin wannan kasa ba abin wasa ba ne, lamuransun wuce dukkan yadda mutum ya ke sawwarawaWallahi.

Ga mu ga Allah! Babu wayo babu dabara! Babu karfibabu iko! Babu mulki babu sarauta! Sai sallallami dasalati.

Allah ya jikan mu.

Cewar Musa Muhammad Dankwano.

Toh Allah Ya Kyauta Zamu So Mu Karbi Ra’ayoyinku A Sashenmu Na Tsokaci Akan Wannan Badakal Da Take Damun Mutanen Arewachin Nigeria, Ta Garkuwa Da Mutane Da Rashin Zaman Lafiya.

Allah Ya Kawo Mana Mafita.

Sannan Kada Ku Manta Ku Danna Alamar Kararrawa Domin Samun Sababbin Shirye-shiryenmu Akoda Yaushe Mungode.

Ku Karanta Wannan Labarin:

Sakamakon katsewar laying wayar MTN kamfani yabada Diya ga duk masu amfani da layinwaya Na MTN na Katin waya da Data.

Ku Karanta Wannan Labarin:

Tirkashi Shugaban ‘yansandan Nigeria yaba da Umarnin a Kamo ‘yansandan dasuke karbar cin hanci a kan titi biyo bayan video da yafita jiya a sabat.

Ku Karanta Wannan Labarin:

Yanzu – Yanzu Akayi Babbar Mutuwar Data Firgita Hankalin Mutane Da Dama innalillahi Matar Abubakar Gumi Ta Rasu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button