Waddannan sune jihohin da suka kasa biyan malaman makaranta albashinsu, jihohin sun hada da Kano, Jigawa, Katsina, Lagos, Ekiti Wanda Hakan yajowo musu
Waddannan sune jihohin da biyan malaman makaranta albashinsu, jihohin Kano, Jigawa, Katsina, Lagos, Ekiti Wanda Hakan yajowo musu

Jigawa na Daya daga Cikin jihohin da suke kasa biyan malaman makarantar kudi.
A wani rahotan da muka Sami daga shafin sawabafm Wanda suntabbatar da wasu manyan shafin jaridar na wasu jihohin da suke kasa biyan malaman makarantar albashinsu.
A wani bincike da jaridar Daily Trust ta buga ranar Asabar, ta gano cewa sabanin wasu jihohin a Najeriya da ke fama da matsalar kasa biyan malaman makaranta albashinsu, jihohin Kano, Jigawa, Katsina, Lagos, Ekiti da ma wasu jihohin gwamnatoci na cika alkawuran da suka dauka na biyan malamai hakkinsu.
Malaman makaranta da kuma wakilan gwamnati a jihohin sun bayyanawa Daily Trust cewa, ana biyan albashin malaman akan lokaci.
Jami’in Hulda da Jama’a na Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano, Malam Aliyu Yusuf ya ce, gwamnatin jihar Kano tana samun nasara wajen biyan albashin malamai yanda ya kamata.
Ya kara da cewa, matsala daya da ake fuskanta ita ce rashin samun damar ciyar da malamai gaba promotion matsalar da gwamnatin ta gada daga gwamnatin baya, amma kuma ya ce, gwamnati ta san da matsalar, kuma kwanannan za a gyara komai.
Wata majiya daga ma’aikatar ilimi ta ce, Gwamna Abdullahi Ganduje da shi da shugabannin kananan hukumomi sun zama daya wajen tabbatar da gudanar kudaden albashin malaman.
“Kun san cewa, kananan hukumomi suna bayara da wani kaso don biyan albashin bayan wanda yake zuwa daga gwamnatin tarayya. A Kano kuma, gwamna ya tabbatar da cewa albashin malaman makaranta shine farko kafin saura.
A jihar Jigawa kuma, Kungiyar Malaman Makaranta NUT reshen jihar ta yabawa gwamnatin jihar wajen biyan malamai albashinsu da sauran hakkokinsu a kan lokaci.
Shugaban Kungiyar, Abdulkadir Yunusa ne ya tabbatar da hakan a wata hira da Daily Trust a ranar Asabar, inda ya kara da cewa akwai tsananin matsalar karancin malaman makaranta a jihar.
Da yake kara tabbatar da matsalar malaman makaranta a jihar, kwamishinan ilimi, kimiyya da fasaha a jihar, Dr. Lawan Yunusa Danzomo, ya ce an mayar da hankali wajen magance matsalar karancin malaman makarantar.
Kwamishinan ya kara da cewa, jihar Jigawa na da adadin malaman makaranta 15,800 gaba daya a fadin jihar.
Ya kara da cewa, gwamnatin jihar ta debe malaman makaranta 6,500 a kwanannan, wadanda suka hada da 1,900 a matsayin cikakkun malaman makaranta da kuma 4,500 a karkashin shirin J-Teach.
To jama’a zamuso muji ra’ayoyinku akan wannan lamarin na kasa bits malaman makarantar a wadannan Jihohi biki daya.
Kada Kumanta a harkulum Kuna tare Dani A Usman Ahmad a shafinmu na Dalatopnews kucigaba da bibiyarmu Domin samin labaran Duniya kaitsaye.
KU KARANTA WANNAN:
Bayyanar Wani Bidiyo Na Adam A Zango Da ‘Yarsa Ya Dauki Hankalin Mutane
Kada Kumanta kudanna Mana alamar kararrawar sanarwa Domin samin Jin kararrawar shirye-shiryanmu masu kayatarwa mungode.